Babban bankin kasar nan CBN ya umarci bankuna da su tura kudaden suka rage cikin asusun bankunan da suka lalace ko aka daina amfani dasu ga wani asusu da ya samar.
Wannan umarni na cikin wata sanarwar manema labarai da bankin ya fitar ranar juma’a mai dauke da sa hannun daraktan dake kula da sashen kudi da daidai tsare tsaren bankuna john Onojah.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ta cikin sanarwa yace dukkanin kudin da masu su basu nema ba kuma suna cikin asusun da aka daina amfani da shi tsahon shekaru 10, za’a killace su a cikin asusun da ya samar mai suna Trust Fund Pool Account.
Daga bisa cbn yace da yuwuwar za’ayi amfani da kudin ne wajen saka jari da kuma inganta harkokin tsaron al’ummar kasar nan.
PRNigeria Hausa











