Home Taska Badaƙalar $1.3m: Kotu ta ba EFCC izinin Kama Tsohuwar Ministar jin ƙan...

Badaƙalar $1.3m: Kotu ta ba EFCC izinin Kama Tsohuwar Ministar jin ƙan Najeriya Sadiya Farouq

Sadiya Farouq

Badaƙalar $1.3m: Kotu ta ba EFCC izinin Kama Tsohuwar Ministar jin ƙan Najeriya Sadiya Farouq

 

Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta ba hukumar yaƙi da masu yi tattalin arzikin ƙasar ta’annuti EFCC, izinin kama tsohuwar ministar jin ƙai ta ƙasar Sadiya Umar Farouq.

EFCC na binciken tsohuwar ministar ne da badaƙalar dala miliyan $1.3m da kuma Naira miliyan N746.6m na ma’aikatar da ake zargin an wawure.

A wani saƙo da EFCC ta wallafa a shafinta na X, ta ce mai shari’a Jude Onwuegbuzie, ya kuma ba da izinin kama sakataren ma’aikatar Bashir Nura Alkali.

Ta ce matakin ya biyo bayan ƙin bayyana a gaban kotu da waɗanda ake zargin suka yi a ranar Alhamis.

Lauyan waɗanda ake ƙarar sun buƙaci a ba su uzuri sakamakon rashin lafiya da hana Sadiya halartar kotun, amma kuma ba a amince da buƙatar tasu ba.

EFCC ta ce ta shigar da ƙarar ce tun a ranar 15 ga watan Disambar 2025, amma ba a samu damar yin ido biyu da waɗanda ake zargin domin miƙa musu takaradar kotun ba.

Sadiya ta riƙe muƙamin ministar ne a mulkin marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, inda daga baya ta auri tsohon babban hafsan sojin saman Najeriya AVM Sadiq Abubakar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp