Gwamnatin Najeriya ta ƙudiri Anyiar Tara N2.5trn Daga Kuɗaɗen Shiga a 2026
Gwamnatin Najeriya ta ƙudiri anyiar samun naira tiriliyan 2.5 na kuɗaɗen shiga na cikin gida a shekarar 2026.
Mukaddashin Shugaban Hukumar Kula da Ɗa’a a Harkokin Kasafin Kuɗi ta Ƙasa, Charles Abana ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa tsakanin shugabannin hukumar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, a Abuja.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A wata sanarwa da mai magana da yawun Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Chris Ugwuegbulam, ya fitar, Mista Abana ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan hukumar ta sa ido kan kuɗaɗen shiga na kusan naira tiriliyan 1.84 da ma’aikatun gwamnati da hukumominta suka samar zuwa watan Satumban 2025.
Ya ce, “Ta hanyar ƙara sa ido kan rarar kuɗaɗen shiga na kamfanonin gwamnati da kuma kuɗaɗen shiga da ma’aikatu da hukumomin gwamnati ke samarwa, hukumar ta lura da kuɗaɗen shiga na kusan naira tiriliyan 1.84 zuwa watan Satumban 2025, kuma yanzu ta ƙudiri aniyar samun naira tiriliyan 2.5 a matsayin kuɗaɗen shiga na shekarar 2026.”












