Home Taska Fasinjoji 18 Sun Mutu a Hatsarin Mota Yayin Dawowa Daga Legas

Fasinjoji 18 Sun Mutu a Hatsarin Mota Yayin Dawowa Daga Legas

Accident

Fasinjoji 18 Sun Mutu a Hatsarin Mota Yayin Dawowa Daga Legas

Wasu Sakkwatawa kimanin mutum 18 sun riga mu gidan gaskiya a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Yauri da ke Jihar Kebbi.

Aminiya ta ruwaito cewa ƙarar kwana ta cimma mutanen ne a yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga Legas, inda suka je suka shafe tsawon lokaci suna neman na kai.

Mamatan dai na cikin fasinjoji 20 da ke cikin wata motar haya mai ɗaukar mutum 18, wadda ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota da misalin ƙarfe 11:00 na daren Litinin, inda mutum 18 suka mutu nan take, yayin da ragowar biyun suka tsira da ƙananan raunuka.

Bello Muhammad, mamba na Ƙungiyar Direbobin Motoci ta Ƙasa (NURTW), kuma abokin direban motar, ya ce shi da wasu abokan aiki ne suka garzaya wurin domin kwaso gawarwakin mamatan bayan sun samu labarin hatsarin.

Ya ce sun isa wurin da misalin ƙarfe 4:00 na asubahin ranar Talata, inda suka tarar motar hayar ta yi mummunan karo da wata babbar mota.

“An kira aka sanar da mu cewa abokin aikinmu ya yi hatsari bayan garin Yauri. Da muka isa wurin, mutum 18 sun riga sun rasu, motar kuma ta tarwatse,” in ji shi.

A cewarsa, an kai gawarwakin zuwa Babban Asibitin Yauri domin tantance su kafin a miƙa su ga iyalansu.

Ya ƙara da cewa shi ne ya tuƙa motar da ta ɗauko gawarwakin mutanen da suka fito daga Gundumar Kajiji zuwa garuruwansu domin yi musu jana’iza.

A cewarsa, mutum ɗaya ne kacal daga cikin fasinjojin ya fito daga Ƙaramar Hukumar Gwandu ta Jihar Kebbi, yayin da sauran 19 ’yan asalin Jihar Sakkwato ne.

Ya kuma ce ɗaya daga cikin mutane biyu da suka tsira shi ne yaron motar, wanda ya yi bankwana da direban kafin su bar Legas.

Muhammad ya ce daga cikin mamatan akwai direban motar, Manniru Sabo, da Basiru Shehu, dukkansu daga ƙauyen Kajiji, da kuma wani mutum daga wani ƙauye da ke ƙarƙashin gundumar.

Ya ƙara da cewa akwai kuma wasu mutum bakwai daga cikin mamatan da suka fito daga ƙauyukan Bingaje da Gudirriga na Ƙaramar Hukumar Yabo, yayin da mutum biyu suka fito daga Ƙaramar Hukumar Gada. Sauran kuma sun fito daga wasu yankuna daban-daban na Jihar Sakkwato.

Bello ya ce ana sa ran za a binne wasu daga cikin mamatan a Yauri saboda yadda gawarwakinsu suka tarwatse, yayin da aka kawo gawarwakin mutanen Kajiji gida, inda aka yi musu jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci.

 

Shi ma Alhaji Shehu Muslim Jabo, makusancin direban motar, ya ce ya taimaka wajen ɗauko gawarwakin zuwa Kajiji sannan ya halarci jana’izar mamatan da suka fito daga Ƙaramar Hukumar Shagari.

Ya ce lamarin ya girgiza al’umma matuƙa musamman la’akari da yadda wasu daga cikin gawarwakin suka tawarwatse ƙwarai.

“Muna cikin matsanancin alhini saboda yadda gawarwakin suka kasance. Wasu ma ba a iya gane su cikin sauƙi,” in ji shi.

Jabo ya yi zargin cewa wata babbar mota mallakin kamfanin Dangote ce ta kauce daga hanyarta ta bugi motar hayar, lamarin da ya haddasa hatsarin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp