Home Taska Gwamnonin Arewacin Najeriya sun Kafa Gidauniyar Yaƙi da Matsalar Tsaro

Gwamnonin Arewacin Najeriya sun Kafa Gidauniyar Yaƙi da Matsalar Tsaro

Gwamnonin Arewacin Najeriya sun Kafa Gidauniyar Yaƙi da Matsalar Tsaro

 

Gwamnonin yankin arewacin Najeriya sun kafa asusun tsaron yankin tare da rantsar da kwamitin amintattun waɗanda za su lura da asusun da jagorantar aiki da kuɗaɗen.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin.

“A yau mun cimma wani muhimman mataki a ƙoƙarin bai-ɗaya da muke yi kan magance ƙalubalen da suka addabi Arewacin Najeriya, musamman matsalar rashin tsaro. A dukkan jihohin Arewa, barazanar ‘yan bindiga, ta’addanci, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran nau’o’in aikata laifuka na ci gaba da kawo cikas ga zaman lafiya.”

Ya ce sun cimma matsaya bayan tarukansu a Abuja da Kaduna cewa yankin na buƙatar wasu matakai na gaggawa, “Duk da cewa gwamnatin tarayya ce ke da alhakin tabbatar da tsaron ƙasa, akwai buƙatar jihohin arewa su ƙara bayar da gudunmawa domin tallafa wa ƙoƙarin hukumomin tsaro na tarayya wajen musayar bayanan sirri da sauransu.”

Ya ce saboda haka ne suka amince da kafa asusun tsaron arewacin Najeriya. “An ƙirƙiri wannan asusu ne domin tattara kuɗaɗe da ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da inganta musayar bayanan sirri da kuma taimaka wa gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro wajen sauke nauyin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.”

Mambobin Kwamitin Amintattu da za a rantsar a yau gwamnamocin jihohin Arewa goma sha tara ne suka zaɓe su bisa cancanta. Dukkansu mutane ne da suka yi fice a fannoni daban-daban na hidima ga ƙasarmu. Muna da cikakken yaƙinin cewa za su kawo ƙwarewa, gaskiya, kishin ƙasa da fahimtar gaggawar wannan aiki.

Gwamna ya ce akwai buƙatar su ƙara ƙaimi wajen magance tushen matsalolin rashin tsaro a yankin da ya ce sun ƙunshi talauci da jahilci da rashin aikin yi da yawan yara da ba sa zuwa makaranta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp