Home Taska China ba za ta Bayar ko ta Sayar wa Iran Makamai ba...

China ba za ta Bayar ko ta Sayar wa Iran Makamai ba a Kowane h Hali – Trump

Donald trump

China ba za ta Bayar ko ta Sayar wa Iran Makamai ba a Kowane 
Hali – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shugabannin China da Rasha, Xi Jinping da Vladimir Putin, sun yi masa alƙawarin cewa ba za su sayar wa Iran makamai ba.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Xi ya tabbatar masa a ganawarsu ta baya-bayan nan a Beijing cewa China ba za ta bayar ko ta sayar wa Iran makamai ba a kowane hali, har da kamfanonin ƙasar.

Trump ya ƙara da cewa shi ma Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi masa irin wannan alƙawari.

Ya ce Putin ya fahimci cewa Amurka ba ta sayar wa Ukraine makamai kai tsaye, sai dai ga ƙasashen ƙungiyar NATO, waɗanda ke biyan cikakken kuɗinsu.

“Kasashen biyu da aka fi dangantawa da Iran, ba na tsammanin suna da hannu. Kuma idan suna da hannu, hakan ba zai kasance cikin maslaharsu ba,” in ji Trump.

A baya-bayan nan kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa hukumomin leƙen asirin Amurka na binciken yiwuwar Rasha ta taimaka wa Iran bayan hare-haren jirage marasa matuƙa da aka kai kan wasu cibiyoyin CIA a yankin Tekun Fasha.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp