Home Taska Jami’an Tsaro Sun Kuɓutar da Mutane 32 Yayin da 4 Suka Mutu...

Jami’an Tsaro Sun Kuɓutar da Mutane 32 Yayin da 4 Suka Mutu a Jihar Sokoto 

Jami’an Tsaro Sun Kuɓutar da Mutane 32 Yayin da 4 Suka Mutu a Jihar Sokoto 

 

Rundunar ƴansandan jihar Sokoto ta sanar da cewa mutum huɗu sun mutu bayan da wasu ’yanbindiga suka kai hari a ƙauyen Maikujera da ke ƙaramar hukumar Rabah a jihar Sokoto.

Rundunar ta ce maharan sun kutsa yankin ne suna harbe-harbe tare da yin garkuwa da mutane da kuma satar dabbobi kafin jami’an tsaro su isa wurin.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce jami’anta tare da haɗin gwiwar dakarun soji sun bazama yankin bayan samun kiran gaggawa cewa ’yanbindiga suna wucewa da shanu da suka sace tare da mutane da suka yi garkuwa da su inda suka toshe hanyoyin da ake zargin ’yan bindigar za su bi wajen tserewa.

Hakan ya janyo musayar wuta mai tsanani tsakanin jami’an tsaro da maharan, lamarin da ya tilasta wa ’yan bindigar tserewa cikin daji tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su da kuma dabbobin da suka sace.

Rundunar ta ce ta samu nasarar kuɓutar da mutum 32 da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba.

Waɗanda aka ceto sun haɗa da maza shida da mata 26, yawancinsu yara ne.

Kwamishinan ƴansandan jihar, Hayatu Hassan Shaffa, ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka mutu tare da jaddada cewa jami’an tsaro na ci gaba da farautar ’yan bindigar domin gurfanar da su a gaban kuliya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp