Home Taska Mutane 15 Sun Mutu a Sabon Harin Yan Bindiga a Jihar Benue 

Mutane 15 Sun Mutu a Sabon Harin Yan Bindiga a Jihar Benue 

'Yan Ta'adda

Mutane 15 Sun Mutu a Sabon Harin Yan Bindiga a Jihar Benue 

 

Makurdi, Benue – Aƙalla mutum 15 ne aka ruwaito sun mutu a safiyar ranar Talata, 28 ga watan Yulin 2026 a wani harin ‘yan bindiga a jihar Benue.

‘Yan bindigan ɗauke da makamai sun kai sabon harin kan kauyukan Ugboju da ke ƙaramar hukumar Otukpo a jihar Benue.

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa harin da aka kai ƙauyen Efeyi-Ugboju ya fara ne da misalin ƙarfe 5:00 na safe a ranar Talata.

Sun bayyana cewa an gano gawarwaki 14 zuwa lokacin da ake tattara wannan rahoto.

Sun kuma ce an kashe mutum ɗaya a ƙauyen Ipom-Ugboju tun da safiyar ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2026.

Ana ci gaba da gano gawarwaki Mazauna yankin sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, domin har zuwa misalin ƙarfe 11:30 na safe ana ci gaba da gano gawarwaki.

Sun ƙara da cewa an garzaya da mutane da dama da suka samu raunuka daban-daban zuwa asibiti domin samun kulawa.

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana lamarin a matsayin abin tausayi.

“Harin ya fara ne da misalin ƙarfe 5:00 na safe kuma ya ci gaba har bayan ƙarfe 9:00. An kashe mutum 14 a Efeyi-Ugboju, sannan waɗanda ake zargi makiyaya ne masu ɗauke da makamai sun kashe wani mutum a Ipom-Ugboju tun safiyar Litinin.” In ji shi

Shugaban ƙaramar hukuma ya tabbatar da harin

Shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya tabbatar da aukuwar harin yayin da yake zantawa da manema labarai a Makurdi.

Ya ce an gano gawarwaki 14 daga Efeyi-Ugboju, yayin da wasu da dama suka samu raunuka. Ogiri ya yi Allah wadai da kisan, yana mai cewa an kai harin ba tare da wata tsokana ba, kuma manufarsa ita ce kashe rayukan mutane marasa laifi.

“Babu wata tsokana. Sun zo ne kawai domin zubar da jini da kashe mutanenmu. An gano gawarwaki 14, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.” “Mutane na rayuwa cikin tsoro, kuma akwai fargaba sosai. Mazauna maƙwabtan al’ummomi ma sun fara tserewa domin neman mafaka.” In ji shi

An nuna damuwa kan rashin tsaro

Shugaban ƙaramar hukumar ya nuna damuwa cewa duk da kasancewar jami’an tsaro, ciki har da sojoji, ‘yan sanda, rundunar MOPOL da Agro-Rangers, hare-haren na ci gaba da faruwa.

“Ban sani ba ko jami’an tsaron da ke wurin ba su isa ba. Ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki na musamman wajen tabbatar da aiwatar da dokar hana kiwo a fili, domin komai yana da alaƙa da wannan.” In ji shi.

A nata ɓangaren, jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Benue (PPRO), DSP Udeme Edet, ta ce har zuwa lokacin ba ta samu cikakken bayani game da harin ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp