Home Taska Kimanin Malamai 200 ne Suka bar Jami’ar KASU – ASUU

Kimanin Malamai 200 ne Suka bar Jami’ar KASU – ASUU

Kimanin Malamai 200 ne Suka bar Jami’ar KASU – ASUU

 

ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) reshen jami’ar jihar Kaduna (KASU) ta ce malaman jami’ar kimanin 200, ciki har da furofesoshi ne suka bar jami’ar sakamakon rashin kyawun yanayin aiki da kuma rashin aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta ƙulla da ASUU a 2025.

Shugaban ASUU-KASU, Dakta Abubakar Abdullahi, ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Litinin, inda ya ce mafi yawan malaman da suka fice sun samu aiki a sabbin jami’o’i da ke ciki da wajen jihar Kaduna.

Ya ce rashin aiwatar da yarjejeniyar, wadda ta fara aiki tun watan Janairun 2026, ya sanya malaman KASU cikin mafi ƙarancin albashi tsakanin ma’aikatan jami’o’i a Najeriya.

ASUU ta bai wa gwamnatin jihar Kaduna da mahukuntan jami’ar wa’adin makonni biyu su fara aiwatar da yarjejeniyar, tare da gargaɗin cewa rashin yin hakan na iya jawo yajin aikin sai baba-ta-gani a jami’ar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp