Home Taska Manyan Hafsoshin Rundunar Kasa da na Sama Sun yi Bikin Karamar Sallah...

Manyan Hafsoshin Rundunar Kasa da na Sama Sun yi Bikin Karamar Sallah Tare da Dakarun su a Fagen Daga… Sun yi Alkawarin Inganta Walwalar Dakarun

Manyan Hafsoshin Rundunar Kasa da na Sama Sun yi Bikin Karamar Sallah Tare da Dakarun su a Fagen Daga… Sun yi Alkawarin Inganta Walwalar Dakarun

Babban hafsan sojin k’asan Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya tare da takwaransa na rundunar sojin sama Air Marshal Isiaka Amao ranar litinin 2 ga Mayu 2022 sun yi bikin k’aramar sallah tare da dakarun fagen daga a Shelkwatar had’ad’d’iyar rundunar arewa maso gabas wato Operation HAD’IN KAI a Maiduguri.

Hafsoshin wad’anda suka gamsu da irin jajircewar dakarun, inda suka yi alk’awarin inganta walwalar su a yayin gudanar da bukukuwan k’aramar sallah.

A jawabin sa Babban hafsan sojin k’asan wanda tun da farko ya ziyarci dakarun da suka samu raunuka a Asibitin Runduna ta 7 inda ya yi alk’awarin samar da kula da lafiyar dakarun a gida Najeriya da kuma kasashen waje. Ya ce za’a koya masu sana’oin hannu domin kare su daga juyayin kwakwalwa.

A sak’on shi na fatan alheri, Babban hafsan sojin sama, ya yi kira ga dakarun had’ad’d’iyar rundunar da su kyautata had’in gwiwa wajen gudanar da ayyukan su. Ya kuma yi masu albishir na samar da sababbin kayayyakin aiki domin inganta yak’in sama.

Wakilin Mai Girma Gwamnan Jihar Borno, kuma mataimakin Gwamnan Jihar, Umar Usman Kadafur a sak’on sa na fatan alheri ya godewa dakarun had’ad’d’iyar rundunar arewa maso domin samar da zaman lafiya a jihar da yankin baki d’aya. Ya bayyana cewa nasarorin da aka samu ya nuna irin jajircewar rundunonin sojin na tabbatar da kawo k’arshen yak’in a yankin.

Birgediya Janar Onyema Nwachukwu
Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Kasan Najeriya
2 Mayu 2022

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp