Babban bankin Nijeriya CBN ya kwace lasisin bankin Haeritage, wanda dakatarwar ta fara aiki nan take.
Wannan na kunshe ta cikin wata takardar sanarwa da mukaddashin daraktan yada labarai ta bankin ta fitar Hakama Sidi Ali, inda tace wannan mataki na zuwa ne bayan da bankin ya karya wasu dokoki na BOFIA.
Ta cikin sanarwa babban bankin na CBN yace bankin ya sabawa sashi na 12 (1) na dokar
Read Also:
“Bankin da hukumar gudanarwasa sun gaza habaka fannin kudin su, wanda ke barazana ga tattalin arzikin kasar nan. Duk da bibiya da CBN yayi domin taimakon bankin, amma bankin Heritage ya cigaba da gudanar da ayyukan sa ba tare da ya dauki matakan gyara ba, A cewar babban bankin na CBN
Domin tabbatar da kwarin gwiwa da gaskiya a fannin harkokin kudi bankin na CBN da hukumar NDIC sun dauki matakin kwace lasisin bankin dogaro da sashe na 12 (2) na dokar BOFIA 2020.
Hakan kuma babban bankin na CBN ya tabbatarwa da ‘yan Nijeriya cewa fannin harkokin kudi zai cigaba da habaka da samun ingantaccen tsaro.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 12 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 53 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com