Gwamantin Kano zata cigada da ayyukan da kwankwaso ya fara

Gwamnatin jihar Kano ta kammala shirin kammala aiyukan titinan karkara mai tsawon kilomita 5 da aka yi watsi da shi a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ba da wannan tabbacin ne a ranar Laraba bayan kammala wani taro da ‘yan kwangilar da ke gudanar da ayyukan a gidan gwamnati.

Ayyukan na kilomita biyar-biyar da aka warewa miliyoyin nairori tsohon gwamna, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ne ya bayar da su a lokacin gwamnatin sa, kuma tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi watsi da su.

Da yake ganawa da ‘yan kwangilar, Gwamna Yusuf ya yabawa musu kan yadda suka amsa kira a kan lokaci, ya kuma ba da tabbacin gwamnatinsa ta kudirci aniyar kammala duk ayyukan da tsohuwar gwamnatin Kwankwaso ta faro don cigaba al’ummar jihar Kano.

Muhimman batutuwan da aka cimma yayin taron sun hada da Komawar yan kwangilar baki aiki nan da mako guda don kammala aikin.

Sauran su ne umarnin gaggawa da aka baiwa ma’aikatar filaye da tsare-tsare ta Jihar domin warware matsalolin da ake fuskanta na biyan diyya.

“An yanke shawarar cewa ‘yan kwangilar za su je bankunan su domin karbar kashi 30 cikin 100 na kudaden da aka ware wa aikin, amma ga wadanda basu karɓi na su tun da farko ba.

“An kuma warware matsalar hauhawar farashin kayayyakin gine-gine da aka samu, inda gwamnati ta amince za ta sake duba farashin sauran kayayyakin da aike aikin da su .

“An kuma amince da cewa gwamnati za ta fitar da tsarin da zata rika biyan yan kwangilar a kowane wata, ta yadda ba za sami tsaiko ba. Don haka aka umarci duk dan kwangilar da ya amince da sabon tsarin da ya koma bakin aiki nan da mako guda ko ya rasa damar”.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 11 hours 29 minutes 23 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 10 minutes 48 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com