Home DUNIYA Kotu ta umarci Sadiya Farouq ta yi bayanin yadda ta kashe biliyan...

Kotu ta umarci Sadiya Farouq ta yi bayanin yadda ta kashe biliyan 729 na tallafi

Babbar kotun tarayyar da ke jihar Legas ta umarci tsohuwar ministar jinƙai, Sadiya Umar Farouk, da ta yi bayanin yadda aka kashe naira biliyan 729 na tallafin da aka raba wa talakawan kasar na tsawon watanni shida.

Cikin hukuncin da ya yanke, mai shari’a Deinde Isaac Dipeolu ya kuma umarci tsohuwar ministar ta wallafa sunaye da bayanan mutanen da suka amfana da tallafin da jihohin da aka raba, da yawan kuɗin da aka raba a kowacce jiha.

Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci da rashawa ce ta shigar da karar Sadiya Farouk a gaban kotun, inda ta buƙaci kotun ta tilasta mata bayar da bayanan, kasancewar kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba ta ‘yancin samun bayanan.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, SERAP ɗin ta ce ta samu kwafin hukuncin da kotun da yi ranar Juma’a.

Alƙalin kotun ya ce kotu ta tilasta wa tsohuwar ministar bayar da bayanan, kasancewa kundin tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadin bayar da bayanai ga kowanne ɗan ƙasa ciki har da SERAP.

”Don haka kotu ta umarci tsohuwar ministar ta yi bayanin yadda ta kashe naira biliyan 729 wajen raba wa talakawan Najeriya miliyan 24.3 a shekarar 2021”, kamar yadda hukuncin ya nuna.

Mai shari’a Dipeolu, ya kuma ce dole ne tsohuwar ministar ta yi wa SERAP cikakkun bayanan hanyoyin da aka bi wajen zaɓo mutanen da suka amfana da tallafin.

Sannan kotun ta kuma umarci ministar ta yi bayanin hikimar biyan naira 5,000 ga talakawan ƙasar miliyan 24.3, wanda adadin kuɗin ya kai kashi biyar cikin 100 na kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2021.

Tun da farko dai lauyan tsohuwar ministar ya buƙaci kotun ta yi watsi da buƙatar ƙungiyar ta SERAP, to sai dai alƙalin kotun bai amince da buƙatar lauyan tsohuwar ministar ba.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Taron Digital PR Summit ya Sanar da Masu Gabatar Da Jawabi 23 a Bugu na 11Tinubu ya Mika Dokoki Biyar ga Majalisar Dattawa Kan Gyaran Hukumar NDLEA, Tsaron Sufuri, da Laifukan YakiTunawa da NIPSS: Lambar Yabo ba Tare da Hikima ba - Hannatu BilyaminuMataƙin Kano Ya Kammala Tseren Ɗinki na Sa'o'i 120 a Kokarin Kafa Tarihin Duniya na Guinness 2027: Dalilin da ya sa Aka Cire Wasu Ƴan Takarar Gwamna Daga Jerin Karshe - INECTunawa da NIPSS: Lokacin da Ka'ida ta Haɗu da Ƙarfi Daga Muhammad Inuwa IbrahimSa'o'i Bayan An Zaɓe Shi a Matsayin Sabon Jarumin Kamfen na APC, Gwamnan Jam'iyyar Accord ya yi Alkawarin Kuri'u Miliyan 1.5 ga TinubuEl-Rufai Ya Kasafta Dala Dubu 600,000 Domin Baiwa Jami'an EFCC, Shaidan DSS Ya Faɗawa KotuAn Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin Mutane
X whatsapp