Akwai Yiwuwar ba zan kai Lokacin Zaɓen 2027 ba – Obi
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya ce akwai yiwuwar ba zai iya kai lokacin babban zaɓe ba domin gwamnati tana yi masa bita-da-ƙulli.
Obi, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin With Chude, wanda mai gabatar da shirye-shirye Chude Jideonwo ke jagoranta.
Tsohon gwamnan Jihar Anambra, ya ce irin matsin da yake fuskanta ya yi yawa har ba zai iya tabbatar da cewa zai kasance a raye domin fafatawa a zaɓen 2027 ba.
“Ba ma batun zama ɗan takara ba ne. Wataƙila ba zan kasance a raye ba. Ina faɗa muku wannan. Duk abin da nake yi domin na rayu, wannan gwamnati tana hana shi. Kuma da gangan take yi,” in ji Obi.
Sai dai Obi ya bayyana cewa yana zargin wani mutum kai-tsaye ba, amma ya ce abubuwan da yake fuskanta suna nuna akwai yunƙurin hana shi gudanar da ayyukansa.
Read Also:
“Ba zargi ba ne. Na sani. Ina fuskantar matsaloli a kullum. Ba za su zo kai-tsaye su ce, ‘muna yin wannan ba,’ amma za ka iya ganin hannunsu a kusan komai,” a cewarsa.
Obi, ya ce abin da yake faruwa ba shi kaɗai ya shafa ba, domin sauran ’yan adawa ma na fuskantar irin wannan matsin lamba.
“Suna matsa wa duk wanda yake adawa da su. Ana kai min hari kai tsaye. Komai,” in ji shi.
Ya kuma kawo misalin wani abin da ya ce ya faru a filin jirgin sama, inda ya zargi jami’ai da kulle masa mota yayin da suka bar sauran motoci.
“Kwanan nan na samu matsala a filin jirgin sama, inda wasu ma’aikata suka zo suka kulle min mota. Na ce musu, ‘Ni ne.’ Amma wanda ke kula da wsjen ya ce bai damu ba.”
Obi, ya ƙara da cewa wasu mutane suna guje wa nuna suna da alaƙa da shi a bainar jama’a saboda tsoron abin da ka iya faruwa da su.
“Ina ganin mutanen da na sani a filin jirgin sama, ba za su gaishe ni ba saboda suna tsoron abin da zai faru da su idan suka yi hakan.”
Ya kuma ce wasu magoya bayansa ma sun kan roƙe shi kada ya halarci wasu bukukuwan iyalansu domin gudun jawo musu matsala.
Har zuwa yanzu, Gwamnatin Tarayya ba ta mayar da martani kan zarge-zargen Peter Obi ba.












