Home Taska Binciken Gaskiya: Shin Gajimaren ne ya ɓulɓulowa ƙasa a Hanyar Abuja Zuwa...

Binciken Gaskiya: Shin Gajimaren ne ya ɓulɓulowa ƙasa a Hanyar Abuja Zuwa Kaduna?

Binciken Gaskiya: Shin Gajimare ne ya ɓulɓulowa ƙasa a Hanyar Abuja Zuwa Kaduna?

 

 

A baya-bayan nan wani abin al’ajabi da ya ɓulla a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna wanda ya ɗauki hankalin matafiya da ke bin hanyar.

Abin mai kama da gajimare ya riƙa ɓulɓulowa daga ƙarƙashin ƙasa, inda yake taruwa ya riƙa tashi sama yana bazuwa a gefe.

Tun a makon da ya gabata ne abun ya fara ɗaukar hankalin matafiya, waɗanda suke sauka daga ababen hawansu tare da shiga cikinsa domin ɗaukar hotuna.

Mutanen da dama dai kan ce gajimare ne ya faɗo a wurin, wani ala’amari da ba a saba gani ba.

Shin gajimaren ne?

Hukumar Kula da Ka’idojin Muhalli ta Najeriya, NESREA, ta ce ta fara bincike domin gano musabbabin ala’amarin.

A ranar Talata ne tawagar jami’an hukumar suka ziyarci wurin da ke kusa da garin Jere a jihar Kaduna domin gane wa idansu.

Cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yaɗa labarai na hukumar, Nwamaka Ejiofor, ta fitar, ta ce jami’an NESREA sun ziyarci wurin domin gudanar da bincike.

Ta kuma ce daga binciken farko da suka gudanar sun gano cewa kumfa ce ke taruwa a wurin ba gajimare ba kamar yadda wasu ke yaɗawa.

Binciken farko da hukumar NESREA ta yi ya nuna cewa wata babbar mota ce ɗauke da wasu sinadarai ta yi hatsari a kusa da wurin, wanda ya janyo zubewar sinadaran da take ɗauke da su.

Kodayake hukumar ba ta tabbatar da ainihin abin da ya haifar da tashin kumfar ba, amma ta ce tana kan bincike domin gano haƙiƙanin abin.

NESREA ta ce ta tattara bayanai daga jami’an gwamnati da mazauna yankin, sannan ta ɗauki samfurin kumfar da ƙasar wurin da kuma ruwan wani rafi da ke kusa domin faɗaɗa bincike.

Hukumar ta kuma gargaɗi jama’a su guji kusantar kumfar da ruwan da ke kusa da wurin da kuma ƙasar da ke kewaye da shi har sai an kammala binciken, domin kauce wa yiwuwar haɗuwa da wani abu mai illa ga lafiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp