Shugaban Amurka ya Yaba wa Shugaba Tinubu Kan Matakan da Yake ɗauka Wajen Yaƙi da Ta’addanci
Shugaban Amurka Donald Trump ya yaba wa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kan abin da ya kira “ƙwazon jagorancinsa” wajen yaƙi da ta’addanci da kuma magance matsalar tsaro a Najeriya.
Fadar shugaban ƙasar ta ce, a cikin wata wasiƙa da Trump ya aike wa Tinubu, ya ce yana yaba wa shugaban Najeriyar kan ƙudurin da yake da shi na magance matsalolin da suka addabi ƙasar, musamman hare-haren da ke shafar al’ummomin Kiristoci.
Trump ya ce babban abin alfahari ne gare shi yana tare da Tinubu wajen yaƙi da ƴan ta’adda domin ƙarfafa Najeriya da bunƙasa ta.
Read Also:
- Mawallafin PRNigeria Ya Fitar Da Littafin Tarihin Rayuwarsa Akan Rigimar NIPSS Yayin Da IMPR Ta Bayyana Cigaba Mai Karfi A Tsakiyar Shekara
- Shugaban Amurka ya Yaba wa Shugaba Tinubu Kan Matakan da Yake ɗauka Wajen Yaƙi da Ta’addanci
- Binciken Gaskiya: Shin Gajimaren ne ya ɓulɓulowa ƙasa a Hanyar Abuja Zuwa Kaduna?
Ya kuma bayyana cewa dangantakar Amurka da Najeriya na da matuƙar muhimmanci a wannan lokaci da rikice-rikice ke ƙaruwa a yammacin Afirka da sauran sassan duniya.
A cewarsa, ƙasashen biyu suna da buri ɗaya na yaƙi da ta’addanci ta kowane fanni, kuma yarjejeniyar haɗin gwiwar tsaro ta shekarar 2026 tsakanin Amurka da Najeriya ta samar da ingantaccen tsarin cimma wannan buri.
Trump ya ce yana alfahari da tura rundunar musamman ta sojojin Amurka domin horas da sojojin Najeriya tare da samar musu da ƙwarewa da kayan aiki da bayanan sirri da za su taimaka wajen kare ƙasar da kuma tabbatar da tsaron ‘yan ƙasa.
A cewar gwamnatin Najeriya ta hannun Bayo Onanuga, daga cikin nasarorin haɗin gwiwar da ƙasashen biyu suka ƙula akwai harin da aka kai ranar 16 ga Mayu kan maɓoyar mayaƙan ISIS a yankin Tafkin Chadi, wanda ta ce ya yi sanadin kashe babban jagoran ƙungiyar Abubakar Al-Minoki da wasu manyan kwamandojinsa.












