Sojojin Najeriya na Neman ɗaya Daga Cikin Jami’inta Ruwa a Jallo, Kan Zargin Sayar wa Ƴan bindiga Kakin Soji
Sashen kula da kayan aiki na rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta ayyana neman ɗaya daga cikin jami’inta ruwa a jallo, saboda zarginsa da sayar da kakin soji ga ”ƴanta’adda da masu aikata laifuka”.
Jami’in sojin wanda kurtu ne, mai suna Mohammed Yusuf Amutu tuni ya tsare daga wurin aikinsa bayan da zargin da ake yi masa ya fito fili.
Cikin wata sanarwar da sashen kula da kayan aikin soji na rundunar sojin ya fitar, ya ce yana ƙoƙarin gano inda sojan yake domin kama shi don fuskantar ladabtarwa.
Read Also:
Rundunar ta jaddada matsayin na rashin lamuntar saɓa wa aiki ko rashin ɗa’a ko duk wani abu da zai janyo wa rundunar sojin ƙasar barazana.
”Duk wani jami’inmu da muka samu da laifin taimaka wa ayyukan ƴanta’adda da masu aikata laifuka ko wasu ƙungiyoyi da gwamnati ta haramta, ta hanyar sayar musu da kakin soji ko wasu kayyaki, to zai fuskanci hukunci ƙarƙashin dokokin soji da kundin tsarin mulkin ƙasa”, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.
Sanarwar ta kuma yi kira ga mutane su taimaka wajen kai rahoton jami’in a duk inda suka ganshi.
”Muna kira ga jama’a duk inda suka ganshi su yi ƙoƙarin sanar da sojoji mafi kusa da su ko wata hukumar tsaro mafi kusa”, in ji sanarwar.










