Home Taska Garkuwa da Mutane: Dakarun Sojin Najeriya Sun Kama Mutane 5 a Jihar...

Garkuwa da Mutane: Dakarun Sojin Najeriya Sun Kama Mutane 5 a Jihar Yobe 

Rundunar Soji

Garkuwa da Mutane: Dakarun Sojin Najeriya Sun Kama Mutane 5 a Jihar Yobe 

 

Dakarun Operation Hadin Kai na rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar maharba sun kama wasu mutane biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ƙauyen Jegalari da ke ƙaramar hukumar Fune a jihar Yobe.

Muƙaddashin jami’in yaɗa labarai na Operation Hadin Kai, Laftanar Mohammed Goni, ya ce an gudanar da wani samame a ranar Alhamis 23 ga watan Yulin 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan waɗanda ake zargin.

“Dakarun Bataliya ta 233 da ke sansanin soji na Damaturu ne suka gudanar da samamen bayan samun ingantattun bayanan sirri kan ayyukan waɗannan da ake zargin,” in ji nsanarwar da ya fitar

Ya ce dakarun sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda uku ƙirar gida, da bindiga pistol guda ɗaya da alburusai iri-iri da kuma wayoyi guda huɗu

Sanrwar ta ce a halin yanzu waɗanda ake zargin suna tsare a hannun sojoji tare da kayan da aka ƙwato domin ci gaba da bincike da kuma tantance rawar da suka taka a ayyukan garkuwa da mutane da sauran laifuka.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da ƙaddamar da hare-haren domin hana ƴan ta’adda da sauran masu aikata laifuka samun damar gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso Gabas

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Garkuwa da Mutane: Dakarun Sojin Najeriya Sun Kama Mutane 5 a Jihar Yobe Sojojin Najeriya na Neman ɗaya Daga Cikin Jami'inta Ruwa a Jallo, Kan Zargin Sayar wa Ƴan bindiga Kakin SojiYaɗa Farfaganda da ƙiyayya Kan Gwamnati ba Zai Kawo ƙarshenta ba - MatawalleMawallafin PRNigeria Ya Fitar Da Littafin Tarihin Rayuwarsa Akan Rigimar NIPSS Yayin Da IMPR Ta Bayyana Cigaba Mai Karfi A Tsakiyar ShekaraShugaban Amurka ya Yaba wa Shugaba Tinubu Kan Matakan da Yake ɗauka Wajen Yaƙi da Ta'addanciBinciken Gaskiya: Shin Gajimaren ne ya ɓulɓulowa ƙasa a Hanyar Abuja Zuwa Kaduna?HRW ta Zargin Hukumomin Najeriya da Rashin Adalci ga Ƴan  ƙungiyar Boko HaramHukuncin da Kotu ta Yanke wa Matashin da ya  Yunƙurin Satar Motar Yan SandaMutane 6 Sun Rasu 4 Sun Jilkata Sanadiyyar Tsawa a Jihar AdamawaMatatar Dangote ta Dakatar da Amfani da Naira Wajen Sayar da Man FeturZaɓen 2027: Jam'iyyar ADC ta Mayar da Martani kan Hukuncin Kotu Akwai Yiwuwar ba zan kai Lokacin Zaɓen 2027 ba - ObiHukuncin da Kotu ta Yanke wa Direban Keke Napep Kan Aikata Fyaɗeɓata Sunan Gwamnatin Katsina: Kotu ta buƙaci Ƴan Sanda su Tsare Dr Kurfi Gwamnonin Arewacin Najeriya sun Kafa Gidauniyar Yaƙi da Matsalar Tsaro
X whatsapp