Home SIYASA Zaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan...

Zaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasa

Zaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasa

 

Jam’iyyar PDP tsagin Kabiru Turaki ta ce ta miƙa sunan tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Tsagin ya bayyana hakan ne ta bakin kakakin kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar, Ini Ememobong, a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.

A cewarsa, rikicin shugabanci da ya dabaibaye PDP bayan hukuncin Kotun Ƙoli ya haifar da kafa kwamitin riƙon ƙwarya domin tafiyar da harkokin jam’iyyar da kuma gudanar da muhimman ayyukanta.

Tsagin Turakin ya nace cewa shi ne halastaccen shugabancin PDP, wanda ya tsayar da Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa tare da sauran ‘yan takarar gwamnoni, majalisun dokoki na tarayya da na jihohi.

Haka kuma ya ce ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke kwanan nan dangane da rikicin shugabancin jam’iyyar.

 

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Tinubu ya yi Umarnin Gaggauta Samar da CNG, ya Sanya Manufa Rage Kudin Mota Daga Oktoba 1NAF Ta Kaddamar da Gidajen Zama 30 a Makurdi Domin Inganta Jin dadin Jami'antaHukumar Kwastam ta Jihar Ogun ta kwace wiwi da Haramtattun Kayayyaki da darajarsu ta kai ₦2.47bnSojojin Sama da na Ruwa Sun Karfafa Hadin Gwiwar Kayayyaki Don Inganta AikiCin Hanci na $500,000: Atiku ya Musanta Laifi, ya Kuma Amince da Cewa ba Laifi ba ne na Tinubu a Shekarar 1993Sojoji da PTDF Sun Tattauna Hadin Gwiwa Kan Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki, Kwarewar Dijital da TsaroHukumar FAAC ta Raba Kudin Shiga N2.338trn ga Gwamnatin Tarayya, Jihohi, Kananan Hukumomi a Watan AugustaMinna: 'Mun Sha Fitsarin Mu Don Rayuwa', Wanda ya Tsira ya Bada Labarin Mutuwar Ma'adinai 37 a Cell Din NSCDCNeja ta Sanya Dokar Hana Zirga-zirga na Sa'o'i 24 Bayan Zanga-zangar Kan Mutuwar Ma'aikatan Hako Ma'adinai 37 a Hannun Jami'an NSCDCShugaba Tinubu ya Fusata, ya Umarci Bincike Kan Mutuwar Mahakan Ma'adinai a Hannun NSCDCGwamnatin Tarayya ta Kafa Kwamitin Mutane 10 Domin Binciken Mutuwar Mahakan Ma'adinai 37 a Hannun NSCDC, ta Dakatar da Jami'ai 21Sojoji Sun Ceto Mutane 6, Sun Kwato Shanu 117 Da Motar Camry a Katsina, ZamfaraSojoji Sun Kawar da Harin Ta'addanci a Gajiram, Mairari, Yayin da Kwamandan JAS da Mayaƙi Suka Mika WuyaNasarar Aikin Hajjin 2026 Alama ce ta Shugabancin Tinubu, In Ji Shettima Yayin Karbar Rahoton NAHCON2027: 'Yan Adawa da Suka Rarrabu Ba Za Su Iya Kayar da Tinubu ba – Kungiya
X whatsapp