Home Taska Abubuwa 5 game da Sheikh Ahmad Gumi

Abubuwa 5 game da Sheikh Ahmad Gumi

Abubuwa 5 game da Sheikh Ahmad Gumi

A ranar Asabar, gobara ta kama gidan fitaccen malamin addinin Musulunci nan mazaunin garin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi.

An tattaro yadda gobarar ta taba kwanon rufin wani bene. Tuni malamin ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce, “yin Allah ne” kuma ba a san me ya haddasa gobarar ba, saboda babu wutar lantarki lokacin da al’amarin ya auku.”

Ga wasu muhimman abubuwa 5 da ya dace a sani game da malamin:

Sheikh Ahmad Gumi shi ne babban dan sanannen malamin addinin Musulunci, kuma tsohon babban alkalin Musulunci na yankin arewacin Najeriya, Abubakar Mahmud Gumi.

An haife shi a watan Oktoba 1960, sannan yana bada fatawa da fassarar Alkur’ani a masallacin Sultan Bello cikin garin Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

Aikin soja Ahmad Gumi ya yi ilimin sakandirin shi a makarantar Sardauna Memorial College (SMC), daga baya ya tafi jami’ar Ahmadu Bello, inda ya karanta likitanci.

Bayan kammalawa, malamin ya wuce Saudi Arabia don cigaba da karatun addinin shi a jami’ar Umm al-Qura, inda ya karanta fassara da tafsirin Alkur’ani mai girma.

Sheikh Gumi ya shiga makarantar horar da hafsoshin soja, inda yayi aiki a sashin lafiya na sojojin Najeriya (NAMC) a matsayin likita, sannan yayi ritaya a kyaftin.

Sulhu da ‘yan bindiga

Tsohon kyaftin na sojojin ya dade ya na shiga labarai, saboda burin sa na ganin an zauna lafiya da tarin ‘yan ta’adda a maboyar su a Kaduna, Katsina da jihar Zamfara.

Wanda yayi kokarin ganin an saki wadanda aka kama, musamman dalibai 27 da aka yi garkuwa da su daga makatantar koyar da gandun dabbobi ta Najeriya a jihar Kaduna cikin watan Maris na shekarar da ta gabata.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Malamin ya sha caccaka daga tarin ‘yan Najeriya, wadanda suka hada da mulkin Buhari saboda irin matsayin shi ga ‘yan bindiga.

Halin sukar Buhari

Sheikh Gumi ya kasance mai matukar sukar gwamnatin kan rashin iya mulki

A shekarar 2019, malamin yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya sauka saboda yadda gwamnatin sa ta gaza.

Ya musanta jita-jita kan cewa yana sukar jam’iyyar APC ne saboda tausayin jam’iyyar adawa ta PDP.

Lokacin da gwamnatin tarayya ta haramta Twitter a shekarar da ta gabata, Gumi ya bukaci gwamnatin tarayyan ta zama mai nuna halin girma wurin amince wa da caccaka.

Ya ce:

“Ya kamata gwamnatin tarayya ta nuna halin girma game da matakan da take dauka, ba za su iya yaki da kafar sada zumunci ba. Ya kamata gwamnatin tarayya ta zamo ginshiki mai amsar kushe.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp