Jerin Lokutan da Adadin Kwanakin da ASUU ta Shiga Yajin Aiki

Jerin Lokutan da Adadin Kwanakin da ASUU ta Shiga Yajin Aiki

 

Yayin da aka tsunduma yajin aikin ASUU na 2022, dalibai za su so sanin yadda ASUU ta fafata da yajin aiki.

Tun shekarar 1999 ASUU ta fara yajin aiki saoda wasu dalilai da ba sa yiwa kungiyar dadi tsakaninta da gwamnati.

A wannan rahoton, mun tattaro muku adadin kwanaki da lokutan da ASUU suka yi yajin daga 1999 zuwa 2020.

Najeriya – Rahoton Punch ya ce ASUU ta shiga yajin aiki. Yayin da kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta shiga yajin aiki a yanzu, dalibai za su san na yi domin ba a san adadin ranakun da kungiyar za ta yi ba kafin ta dawo.

Daga shekarar 1999 zuwa 2020, kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki sau 15, lamarin da ya jawo tsaiko ta wasu bangarorin ilimi ga daliban jami’a.

A duk wadannan lokuta, ASUU na samun tasgaron wata bukata ce daga gwamnatin tarayya, wanda ya rage mata babu zabin da ya zarce shiga yajin aiki domin neman sulhu cikin sauki.

A yau, 14 ga watan Fabrairu, kungiyar ta sake shiga wani yajin saboda gazawar gwamnatin wajen biya mata bukata kamar yadda aka saba, inji ta.

Teburin jerin yajin aikin ASUU legit.ng Hausa, ta tattaro daga majiya lokutan da ASUU ta shiga yaji tun daga 1999 har zuwa 2020, kamar yadda The Cable ta tattara.

Ga jerin kamar haka:

1.Shekarar 1999 – Kwanaki 150
2.Shekarar 2001 – Kwanaki 90
3.Shekarar 2002 – Kwanaki 14
4.Shekarar 2003 – Kwanaki 180
5.Shekarar 2005 – Kwanaki 14
6.Shekarar 2006 – Kwanaki 3
7.Shekarar 2007 – Kwanaki 90
8.Shekarar 2009 – Kwanaki 8
9.Shekarar 2009 – Kwanaki 120
10.Shekarar 2010 – Kwanaki 157
11.Shekarar 2011 – Kwanaki 59
12.Shekarar 2013 – Kwanaki 165
13.Shekarar 2017 – Kwanaki 35
14.Shekarar 2018 – Kwanaki 94
15.Shekarar 2020 -Kwanaki 120

Bayan barazana da kai ruwa rana, a yau ASUU ta sake shiga yajin aiki, sai Allah yasan ranar dawowarsu.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 14 hours 11 minutes 16 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 15 hours 52 minutes 41 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here