Home SIYASA Ba zan mayar da wani yanki na Nijeriya saniyar ware ba –...

Ba zan mayar da wani yanki na Nijeriya saniyar ware ba – Tinubu

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi alƙawarin yi wa ƙasa ayyukan ci gaba daidai-wa dai da ba tare da nuna wariya ga wani ɓangare ba.

Asiwaju Tinubu, wanda za a rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a ranar 29 ga Mayu, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar yana ziyarar kwanaki biyu ne a jihar domin ƙaddamar da ayyukan da gwamnatin Nyesom Wike ta aiwatar.

“Ba zan mayar da wani yanki saniyar ware ba, amma zan bar ayyukan da ba za a manta da su ba a faɗin Nijeriya,” in ji shi a yayin buɗe gadar Rumuokwuta/Rumuola.

Tinubu ya yabawa Gwamna Wike bisa ayyukan ci gaba da ya cimma a jihar Ribas, musamman gadar sama 12 da aka gina a faɗin babban birnin jihar, inda ya ce lallai tarihi zai riƙa tunawa da shi.

Ya ce da irin nasarorin da ya samu a jihar, Nijeriya za ta buƙaci gwamnan Ribas ɗin mai barin gado a manyan muƙamai.

A ɓangaren siyasa, Tinubu ya godewa Wike da al’ummar jihar Ribas bisa goyon bayan da suka ba shi.

Ya ce yana jihar ne bisa alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe a Ribas, inda ya ce “idan ka yi alƙawari, ka cika shi.

“Ba zan taɓa mantawa da muhimmiyar rawar da manya da kuma al’ummar jihar nan suka taka ba a yaƙin neman zaɓen da na yi na zama shugaban ƙasar nan. Kuna da godiyata ta har abada.

“A mai girma Gwamna Wike, na ga mutum mai ƙa’ida. Ya ɗauki matakin da ya dace na cewa a mayar da shugabancin ƙasarnan Kudu, kuma ya samu ƙwarin guiwar jajircewa kan matsayarsa, ba tare da la’akari da wa hakan zai ɓatawa ba.

“Haƙiƙa shi mutum ne mai mutunci. Bai zaɓi biyan buƙatar kansa ba, a’a, ya zaɓi biyan buƙatar ƙasa da al’ummar jihar Ribas, ina gode masa bisa wannan jagorancin na sadaukar da kai,” inji shi.

A nasa jawabin, Wike ya ce gayyatar da aka yi wa Tinubu domin ƙaddamar da ayyuka a jihar cika alƙawari ne da aka yi a ziyarar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Ribas.

Ya kuma godewa Tinubu kan yadda ya amince ya ziyarci jihar Ribas tare da ƙaddamar da ayyukan.

Wike, wanda ya caccaki shugabannin jam’iyyarsa ta PDP, ya yaba da zaɓen Tinubu wanda a cewarsa, ya kunyata masu zagon ƙasa.

Taron ya samu halartar Kakakin majalisar wakilai Hon. Femi Gbajabiamila da Gwamna Abubakar Badaru (Jigawa), David Umahi (Ebonyi), Abdulrahman Abdulrazaq (Kwara), Seyi Makinde (Oyo) da Hope Uzodinma (Imo).

Sauran sun haɗa da tsoffin gwamnoni Dr Peter Odili (Ribas), Cif Bisi Akande (Osun), Cif James Ibori (Delta), Dr Kayode Fayemi (Ekiti), Cif Timipre Sylva (Bayelsa) da Cif Ayo Fayose (Ekiti).

Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ribas, Mista Sim Fubara, Ministan matasa da ci gaban wasanni, Mista Sunday Dare, Mista Dele Alake da kuma Alhaji Kashim Ibrahim Imam, da dai sauransu.

Ofishin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa
Abdulaziz Abdulaziz
Mayu 3, 2023

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Darakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da Wiwi
X whatsapp