Home Taska ‘Yan Bindiga sun Kashe Fasto da Iyalansa a Jihar Plateau

‘Yan Bindiga sun Kashe Fasto da Iyalansa a Jihar Plateau

'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga sun Kashe Fasto da Iyalansa a Jihar Plateau

 

Jihar Plateau – ‘Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Gako da ke ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Plateau.

‘Yan bindigan sun kashe wani fasto da wasu daga cikin iyalinsa guda uku a yayin harin da suka kai a cikin dare.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa mummunan lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 26 ga watan Afirilun 2027.

‘Yan bindiga sun kashe fasto da iyalansa

Waɗanda abin ya shafa an bayyana sunayensu kamar haka, Fasto Ayuba Choji, matarsa Chundung Ayuba, da kuma yayansu biyu, Cyril Ayuba da Endurance Ayuba.

Maharan sun far wa ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare, inda suka harbi ba kakkautawa.

Wata mazauniyar yankin, Martha Dalyop, ta shaida wa manema labarai cewa ƙarar harbin bindigar ya tursasa wa mazauna garin gudu don tsira da rayukansu.

Mutane na barin gidajensu a Plateau

Ta yi kukan cewa hare-haren da ake yawan kai wa sun ci gaba da jefa al’ummomi cikin tsoro, har ta kai da da yawa ba sa iya kwana a gidajensu ko kula da gonakinsu.

Jaridar The Punch ta ce yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar matasan Berom, Rwang Tengwong, ya siffanta lamarin a matsayin abin ban tsoro.

“Wannan hari na baya-bayan nan ya nuna cewa maharan yanzu suna kai hari ne a wuraren shaƙatawa, yankunan manoma, da kuma jami’an tsaro na ‘yan sa-kai da ke kare karkara.”

– Rwang Tengwong

‘Yan bindiga sun rarrabu yayin harin Ya yi zargin cewa maharan sun rarraba kansu gida-gida ne yayin gudanar da aikin, inda wasu suka kai hari kan mazauna gari, wasu suna lalata gonaki, yayin da wani rukunin ke yin sintiri ko tare hanyoyi don hana mutane tserewa ko samun taimako. ]

Haka kuma, Tengwong ya bayyana cewa maharan sun lalata gonakin kabeji, barkono, da masara da dama a garin Kassa da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi a cikin sa’o’i 48 da suka gabata.

Wannan sabon lamari ya ƙara ruruta wutar fargaba a faɗin Riyom da maƙwabciyarta Barkin Ladi, inda mazauna yankin ke kiran hukumomin tsaro da na gwamnati da su tsananta ƙoƙari don dakatar da kashe-kashe da lalata hanyoyin samun abinci a jihar.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Kakakin rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Oteh, da na rundunar ’yan sandan jihar Plateau, SP Alabo Alfred, ba su amsa saƙon da aka aika musu ta WhatsApp ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Al’ummar Berom sun sha zargin Fulani makiyaya da alhakin kai waɗannan hare-haren, amma shugaban ƙungiyar MACBAN na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya sha musanta waɗannan zarge-zargen, yana mai dagewa cewa mambobinsa ba su da hannu a hare-haren da ake kai musu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp