An Ceto Marayu 15 Daga Hannun ƴan Bindiga a Jihar Kogi
Wasu ƴan bindiga sun sace yara 23 da mai ɗakin shugaban makaranta da gidan marayu na Dahallukitab da ke Zariagi, wani ƙauye da ke Kabba a kan titin Lokoja zuwa Okene da ke ƙaramar hukumar Adavi a jihar Kogi.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kingsley Fanwo ya fitar a yau Litinin, ya ce an sace yaran ne a daren ranar jiya Lahadi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya kuma ce jin kaɗan bayan samun rahoton harin, ƴan sanda tare da goyon bayan wasu jam’ain tsaro suka isa yankin, inda suka yi nasarar ceto yara 15.
Gwamnatin jihar na Allah-wadai da harin, inda ta bayar da tabbacin cewa jami’an tsaro na ci gaba da aiki wajen ceto sauran mutanen.
Sai dai sanarwar ta bayyana cewa makarantar wadda kuma take aiki a matsayin gidan marayu ba ta da rajista, inda ya ce irin waɗannan makarantu da ke irin waɗannan yankunan kuma gwamnati ba ta san da su ba, na kasancewa cikin barazana musamman a wannan lokaci na rashin tsaro.












