Shugaban NITDA ya Gudanar da Ziyarar Sallah a Mahaifarsa, Haɗejia

Mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), ya gudanar da ziyarar barka da sallah a mahaifarsa, (Haɗejia).

Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A jiya rana ta farko, ya karɓi baƙuncin al’umma daban-daban a gidansa, kana kuma ya ziyarci ƴan’uwa da abokan arziƙi a gidajensu ya yi musu barka da sallah, haka zalika kuma ya kai ziyarar gaishe-gaishe da ta’aziyya ga mutanen da aka yi wa rashe-rashe a wurare daban-daban inda ya gabatar da addu’ar Allah Ya ji ƙansu, Ya kuma ba wa duk iyalai ƴan’uwa da dangi haƙuri.

Talata, 3 ga watan Maris, 2022.












