Home General Masu sa ido kan zaɓe daga ƙasashen renon Ingila sun isa Najeriya

Masu sa ido kan zaɓe daga ƙasashen renon Ingila sun isa Najeriya

Masu sa ido a zaɓe daga ƙasashen renon Ingila sun iso Abuja, babban birnin Najeriya, gabanin babban zaɓen ƙasar na shugaban ƙasa da kuma ‘yan majalisar tarayya a ranar Asabar.

Kungiyar ta kunshi mutum 16 da suka fito daga ƙasashen renon Ingila wanda ya kunshi ‘yan siyasa da jami’an diflomasiyya da masana bangaren shari’a da masu kare hakkin ɗan adam da kuma daidaiton jinsi.

Da yake jawabi ga manema labarai a yau Litinin, shugaban kungiyar wada kuma shi ne tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Thabo Mbeki, ya ce kudurinsu shi ne sa ido da kuma duba shirin da aka yi kafin zaɓe da ayyukan ranar zaɓe da kuma bayan zaɓe.

Mista Mbeki ya lura da cewa zaɓukan Najeriya za su kasance manya a nahiyar Afirka kuma sakamakonta na da matukar muhimmanci ga ɗaukacin nahiyar.

A don haka ya buƙaci jam’iyyun siyasa a ƙasar da ‘yan takara da kuma magoya bayansu da su tabbatar da ganin an yi zaɓukan ranar 25 ga watan Febrairu cikin koshin lafiya da kuma gaskiya.

An kiyasta cewa mutum miliyan 93.4 ne suka yi rajista domin samun damar kaɗa kuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya a cikin rumfunan zaɓe 176,846 da ke faɗin Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp