Adamawa: Ayyana Zaɓen Gwamna a Matsayin Wanda bai Kammala ba shi ne Daidai – Binani
‘Yar takarar kujerar gwaman jihar Adamawa ƙarƙashin jam’iyyar APC Sanata Aishatu Ahmed Binani, ta bayyana goyon bayanta kan matakin hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗauka na bayyana zaɓen gwaman jihar a matsayin wanda bai kammala ba.
Yayin da ta bayyana a cikin shirin ‘Politics Today’ na gidan talbijin ɗin Channels Tv, Sanata Aishatu Binani ta yi maraba da matakin, inda ta yi zargin cewa an aikata kura-kurai da rikice-rikice a wasu ƙananan hukumomin jihar.
Read Also:
Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen jihar Farfesa Muhammadu Mele na jami’ar Maiduguri ne ya ayyana sakamakon zaɓen gwaman jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba.
Gwaman jihar mai ci Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ke neman wa’adin mulkin jihar karo na biyu ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’u 421,524, yayin da ita kuma Sanata Binani ta jam’iyyar APC ke da yawan ƙuri’u 390,275.
Jami’in zaɓen ya bayyana cewa ba a gudanar da zaɓen a rumfunan zaɓe 69 a faɗin jihar ba, kuma adadin katunan zaɓen da aka karɓa a duka rumfunan sun kai 37,016, wanda kuma adadinsu ya zarta tazarar ƙuri’u 31,249 da ke tsakanin ‘yan takarar biyu.
Sanata Aishatu ta ce ”matsayina game da matakin shi ne jami’in tattara sakamakon zaɓen jihar ya yi daidai da ya bayyana sakamakon zaɓen jihar a matsayin wanda bai kammala ba’
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 48 minutes 38 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 30 minutes 3 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com