A Najeriya, majalisun yakin neman zabe na jam’iyyar APC da na PDP sun kalubalanci hukumar tsaro ta DSS ta yi wa wadanda suke kitsa munakisar samar da gwamnatin rikon kwarya a kasar dirar mikiya.
A mabanbantan ganawa da suka yi da wata jaridar kasar a ranar Laraba a Abuja, sun ce neman samar da gwamnatin rikon kwarya abu ne da ya saba wa doka, saboda haka kamata ya yi a kama duk Wanda yake da hannu a lamarin.
Read Also:
Sun bayyana haka ne biyo bayan sanarwar da huukumar tsaron DSS din ta fitar, wadda ke cewa wasu mutane na kulla munaakisar samar da gwamnatin rikon kwarya a Najeriya.
Tun da farko hukumar DSS ta fada a wata sanarwa da ta samu sa hannun kakakinta Peter Afunanya cewa wasu ‘yan siyasa a Najeriya na kokarin dakile rantsar da zababben shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.
Dan takarar APC ne dai ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuri’u 8,794,726 inda ya doke abokin hamayyarsa na PDP, Atiku Abubakar, wanda ya samu kuri’u 6,984,520 da Peter Obi na jam’iyyar Labour mai kuri’u 6,101,533.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 21 minutes 38 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 3 minutes 3 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com