Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya amince da nada Alhaji Habu Muhammad Fagge a matsayin shugaban hukumar kula da ‘yan fansho ta jihar Kano.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Nadin ya fara aiki ne nan take kamar yadda gwamnan ya bayar da umarnin mikawa tare da karbar ragamar mulki cikin sa’o’i 24 da wannan sanarwar.Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar aka taba ga manema a jihar.
Alhaji Habu Fagge, wanda ya kammala karatunsaa A harkokin Kudi daga Jami’ar Abraham Lincoln, ya yi wa’adi biyu a matsayin Shugaban Hukumar karɓar haraji ta jihar kano.
Ya rike mukamai daban-daban a ma’aikatun gwamnatin jihar Kano da suka hada da daraktan kudi, daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga da darakta akan harkokin da suka shafi haraji.
PRNigeria hausa












