Rahotannin na Daga Nijeriya na bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu yana ganawar sirri da tsohon gwamnan jihar kano Rabiu Kwankwaso wanda ya yiwa jam’iyyar (NNPP) takarar shugaban kasa.
Kwankwaso, wanda tsohon Ministan Tsaro ne, Kuma suna da kyakyawar alaka da Tinubu, wanda a lokuta daban-daban ya bayyana shugaba mai ci a matsayin wanda yasan dabarun iya mulki.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Idan dai za’a iya tunawa PRNigeria hausa ta ruwaito cewa a kwanakin baya kafin rantsar da shugaban ƙasar sai da Kwankwaso suka gana da shugaban ƙasar a birnin faransa.
Sai dai ganawar Tinubu da Kwankwason ta jawo cheche-chekuche a jihar kano, musamman yadda aka tsinkayi wata murya da ake zargi ta tsohon gwamnan kano Ganduje yana kokawa game da ganawar Tinubu da Kwankwason.
PRNigeria hausa












