Ko za’a koreni sai na fadi gaskiya kan Tinubu – Ndume

Dan majalisar dattijai mai wakiltar Borno ta Kudu Sanata Ali Ndume ya ce zai ci gaba da faɗa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu gaskiya, ko da hakan zai janyo masa kora daga jam’iyyar.

Sanata Ali Ndume ya ce: “Kowa ya san abin da ke faruwa a ƙasar nan. Kowa yana ji a jikinsa. Kuma ba laifi ba ne in gaya ma shugaban ƙasa don a kawo gyara”.

Sai dai ga dukkan alamu, ko Shugaba Tinubu bai ga laifin waɗannan kalamai ba, to ran jam’iyyarsa ta APC ya ɓaci, abin da ya sanya ta fitar da sanarwa tana yi wa Sanata Ndume gargaɗi.

APC ta bayyana cewa Ali Ndume, babban ɗan jam’iyya ne kuma sanata sannan yana da ƙima sosai a idonta da kuma jama’a, don haka in ji ta, bai kamata duk lokacin da za a ambace shi, sai a ce ya yi wani abu da zai tozarta jam’iyya ba.

An ambato sanatan a baya-bayan nan yana iƙirarin cewa Shugaba Bola Tinubu yana zagaye da mashawarta waɗanda ba nagari ba, ko kuma ƴan hana ruwa gudu da ke toshe hanyar da za a je, a ba shi shawara tagari.

“Ko kuma su suke ba shi shawarwari waɗanda ba nagari ba, yake aiki da su,” kamar yadda mai magana da yawun APC, Mallam Bala Ibrahim ya shaida wa BBC.

A watan Yulin da ya wuce ma, sai da jam’iyyar APC ta nemi Majalisar Dattijai ta tuɓe Sanata Ndume daga muƙaminsa na mai tsawatarwa a majalisar saboda zargin sukar gwamnatin Shugaba Tinubu.

Daga bisani dai sanatan ya nemi afuwa, amma har yanzu ba a mayar da shi kan muƙamin mai tsawatarwar ba.

Sanata Ndume ya ce yana magana ne a bainar jama’a saboda ba ya samun damar ganin shugaban ƙasar, balle ya je ya faɗa masa halin da al’ummar Najeriya ke ciki.

“Na rubuta sau biyu, na yi ma wa’anda suke kusa da shi magana. Kuma maganan da na yi gaskiya ne, kundin mulkin ƙasa ya ba ni damar haka.”

A cewarsa, haƙƙi ne a kansa, ya ba da shawara a matsayinsa na dattijo.

APC dai ta ce babba mai ƙima kamar Ali Ndume, bai kamata a ce ana yamaɗiɗi da sunansa a matsayin wanda ke ƙoƙarin tozarta martabar jam’iyya ba.

Amma Ndume ya ce a duk bayanansa babu inda ya aibata wani, kuma babu inda ya soki jam’iyya ko shugaban ƙasa.

Ya ce duk maganar da ake yi matuƙar dai game da shawara ce, to yana nan a kan matsayinsa.

Sanatan ya ce ya bi duk hanyar da zai iya bi don ganin ya samu damar ganin shugaban ƙasar saboda ya bayyana masa halin da ƴan Najeriya ke ciki amma bai yi nasara ba.

“Maganar cewa ni babban ɗan jam’iyya ne wanda zan iya ganin shugaban ƙasa, ba haka ba (ne).”

Ya ce yana magana ne domin sauke nauyin al’umma da ke kansa a matsayinsa na mai wakiltar jama’a.

A baya-bayan nan dai al’ummar Najeriya sun sake shiga cikin matsin rayuwa bayan kamfanin samar da man fetur na NNPCL ya ƙara sanar da ƙarin kuɗin litar man fetur.

Ƙarin na kimanin kashi 15, shi ne na biyu a tsawon wata guda.

Tun tuni da ma tashin farashin man fetur ya haddasa hauhawar kuɗin kayan masarufi a ƙasar abin da ya sanya magidanta da yawa a Najeriya cikin mawuyacin hali.

Ali Ndume dai ya yi iƙirarin cewa wasu makusanta sun tokare Tinubu kuma sun hana shi sanin mawuyacin halin da ƴan ƙasar suke ciki.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 11 hours 21 minutes 53 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 3 minutes 18 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com