Home Taska An Gurfanar da Mutane 24 Bisa Zargin Kashe Matar Aure a Maraban...

An Gurfanar da Mutane 24 Bisa Zargin Kashe Matar Aure a Maraban Jos

An Gurfanar da Mutane 24 Bisa Zargin Kashe Matar Aure a Maraban Jos

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta gurfanar da mutum 24 a gaban kotun majistare bisa zarginsu da hannu a kisan wata matar aure da wasu fusatattun mutane suka yi a Maraban Jos.

Ana tuhumar waɗanda ake zargin da laifukan bayar da gudummuwa wajen aikata laifi, tayar da hankalin jama’a, lalata dukiyoyi, lalata kadarorin gwamnati da na ‘yan sanda, da kuma kisan kai.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ta jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar ta ce an gurfanar da su ne bayan binciken da ‘yan sanda suka gudanar kan lamarin da ya faru a ranar 21 ga Yunin 2026, lokacin da aka kashe matar “bayan mutanen sun ƙwace ta daga hannun ‘yan sanda.”

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 ga Yulin 2026, inda kotun ta bayar da umarnin a tsare dukkan waɗanda ake zargin a gidan yari har sai an kammala shari’ar.

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ƙara da cewa har yanzu ana ci gaba da binciken fiye da mutum 100 da ake zargin su da hannu a lamarin, tare da alƙawarin gurfanar da duk wanda bincike ya nuna yana da laifi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Tinubu Ya Kaddamar da Jiragen Helikwafta Biyar na NAF Yayin da Rundunar ke Jiran Karin Jiragen 67NSA Ya Bawa Kwamitin Bita Dokar Tsaron Kasa Wa'adin Makonni HuduINEC Za Ta Iya Tabbatar da Pantami a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Gombe na PDPCikin Juyin Juya Halin Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa na Dr Aliyu a ICPC, Daga Nafisat BelloKwankwaso Ya Yi Gargadi Kan Hotunan AI a Rijistar INECBayan Fagen Yaƙi: Me Yasa Sadarwa a Lokacin Rikici ta Zama Wajibi ga Tsaron Ƙasa Daga MUKHTAR Ya'u Madobi Kungiyar Tinubu ta Kaddamar da Dandali Domin Kara Muryar Ƴan KasaHukumar PSC ta Ƙara wa Jami'anta 2 Muƙamin DIG, 10 AIG, 17 CP da Sauran 3,850Gara Gombe Ya Dakatar da Ayyukan Al'umma Bisa Zargin Tsangwamar SiyasaRahoton Siyasa: ADC ta Haifar da Muhawara Kan Ranar Zaɓe Yayin da APC Ke Jagorantar Ganuwa, NDC na da Kashi 68.7%Sojoji Sun Kwato Dabbobi 520 da Aka Sace, Sun Ceto Makiyaya 2 a SokotoTinubu ya Umarci EFCC da ta bi Diddigin Rabon Kuɗaɗen FAAC na Jihohi da Ƙananan HukumomiFilato: Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi da Kashe Makiyayi a ManguUmrah: Tinubu Zai Tafi Saudiyya ya Dawo Mako Mai ZuwaNITDA, NCC Sun Nemi Ƙarfafa Tsaron Yanar Gizo Yayin da AI ke Sauya Barazanar Dijital
X whatsapp