Hukuncin da Kotu ta Yanke wa Direban Keke Napep Kan Aikata Fyaɗe
Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa wani direban Keke Napep, Michael Effiong Japhet, hukuncin ɗaurin rai da rai bayan ta same shi da laifin aikata fyaɗe da kuma sata.
Mai shari’a Archibong Archibong, ya ce kotun ta gamsu da hujjojin da masu gabatar da ƙara suka bayar, inda ta tabbatar da cewa Japhet ya aikata laifukan da ake zargin sa da aikatawa.
Read Also:
Kotun ta yanke masa hukuncin ne bisa dokar laifukan fyaɗe ta Jihar Akwa Ibom ta shekarar 2000, bayan an same shi da laifin yi wa wata mata fyaɗe da kuma ƙwace mata kuɗi.
An bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 23 ga watan Fabrairun 2015, lokacin da Japhet ya ɗauki wata mai sayar da kayan marmari daga Ekom Iman zuwa Iko Ofon a Ƙaramar Hukumar Ikono.
A maimakon kai ta inda ta nufa, an ce ya sauya hanya ya bi da ita zuwa wani waje da ba kowa, inda ya yi mata fyaɗe.
An kuma zarge shi da ƙwace jakarta mai ɗauke da kuɗin cinikinta na ranar Naira 7,000, duk da roƙon sa da ta yi kada ya cutar da ita.
Kotun ta ce bayan sauraron dukkanin shaidun, ta samu Japhet da laifin da ake tuhumarsa da shi, sannan ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.












