Jam’iyyar NDC ta Buƙaci Sanata Hanga da Gaya da su Sake Tunani Kan Sauya Sheƙa
Jihar Kano – Jam’iyyar NDC ta bukaci Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga, da tsohon gwamnan Kano, Kabiru Ibrahim Gaya, da su sake tunani kan rade-radin da ke cewa suna shirin komawa jam’iyyar APC.
Kiran ya biyo bayan ziyarar da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, tare da Hanga da Gaya suka kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ranar Lahadi, 26 ga watan Yuli, 2026.
Jaridar Punch ta wallafa yadda shugaban APC na kasa ya kai ziyara gidajen Hanga da Gaya, lamarin da ya kara tayar da jita-jitar cewa suna dab da sauya sheka.
Kiran NDC ga Hanga da Gaya Shugaban NDC na jihar Kano, Hussaini Isah Mairiga, ya shaida wa Daily Trust cewa jam’iyyar ta damu da rahotannin da ake yadawa kan sauya shekar manyan siyasar biyu.
Ya ce:
“Labarin cewa APC mai mulki na kokarin jan hankalin Sanata Rufai Sani Hanga da tsohon gwamnan Kano Kabiru Gaya ya bazu ko’ina.
Read Also:
Har yanzu ba su sanar da mu a hukumance cewa za su sauya sheka ba, amma jiya ma mun gan su sun ziyarci Shugaba Tinubu. Wannan na nuna cewa labarin na iya zama gaskiya.”
Mairiga ya ce jam’iyyar ba za ta ji dadin rasa irin wadannan manyan jiga-jigai ba saboda haka su yi hakuri, su yi zamansu a NDC.
Ya kara da cewa:
“A matsayinmu na shugabanni, ba za mu yi farin ciki idan suka sauya sheka ba. Ko mamba na gari ya fita ba ma jin dadi, balle irin wadannan manyan mutane. Muna da kyakkyawar alaka da su kuma muna girmama juna.”
NDC ta roki su Hanga Mairiga ya amince cewa Hanga ya taba nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake tafiyar da wasu al’amura a cikin NDC, amma ya ce jagoran jam’iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zabi kada ya mayar masa da martani nan take.
A cewarsa:
“Tun da ba su sanar da sauya shekar ba a hukumance, muna rokon su su sake tunani su dakatar da wannan shiri. Mu zauna mu tattauna idan akwai abin da muka yi musu ba daidai ba.” “Kwankwaso ya ce bai ba shi amsa ba ne saboda yana cikin fushi, don haka ya jira ya huce kafin su zauna su tattauna.” Duk da kusancin da jam’iyyar APC mai mulki ke nunawa Sanata Hanga da Gaya, shugaban NDC na Kano ya ce har yanzu mutanen biyu cikakkun ƴaƴanta ne.












