Dakarun Ukraine Sun Daƙile Harin Sojojin Rasha a Birnin Kharkiv
Dakarun Ukraine sun ce sun daƙile harin sojojin Rasha a garin Kharkiv na biyu mafi girma a ƙasar bayan ƙazamar fafatawa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Gwamnan yankin, Oleh Synehubov, ya ce yanzu an fatattaki dakarun na Rasha daga garin bayan gumurzun da suka yi a kan tituna.
Dubban mutane ne suka kwana a gidajen ƙarƙashin ƙasa, yayin da wani mazaunin garin ke siffanta yanayin da wani fim ɗin Amurka mai suna Star Wars.
“Wata fashewa mai mugun ƙara ta sa kunnuwana sun motsa,” a cewar wani.











