Miyagun ƙwayoyi da Makamai: Jami’an Tsaro Sun Kama Mutane 8 a Jihar Yobe
Rundunar ’yan sandan jihar Yobe ta kama mutane takwas bisa zargin laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi, sannan ta ƙwato makamai da dama a sassa daban-daban na jihar.
Kamen waɗanda ake zargi, ya biyo bayan ci gaba da tsare-tsaren hana aikata laifuka da kuma daƙile su ta hanyar yin sintiri mai ƙarfi, da kai samame a maɓoyar masu laifi da wuraren ɓatagari da ’yan sanda ƙarƙashin jagorancin leƙen asiri a faɗin jihar ke yi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ne ya bayyana hakan, inda ya ce baya ga waɗannan ƙoƙarin, sabuwar rundunar da aka kafa a ƙarƙashin sabon sashin mayar da martani kan laifuka ( VCRU), makonni biyu bayan ƙaddamar da ita, ta fara gudanar da ayyuka na dare da rana kuma ta samu ci gaba tare da kama mutane takwas da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da kuma waɗanda ake zargi da aikata laifuka masu tayar da hankali.
Read Also:
Ya ƙara da cewa, “A ranar 9 ga Yuni, 2026, da misalin ƙarfe 18:00 na safe, jami’an rundunar VCRU, waɗanda ke aiki bisa bayanan sirri sun gudanar da wani samame a sanannen sansanin ’yan sanda na New Marte Ghetto da ke Damaturu.”
Ya ce, an kama Usman Hassan, wanda aka fi sani da Bapani, mai shekara 20, da ke da tarin wiwi da kuma tarin takardun rubutattu na ɗaliban Jami’ar Jihar Yobe.
An kuma kama Bukar Sale, wanda aka fi sani da Benzima, mai shekara 18, ɗauke da wasu miyagun ƙwayoyi da kuma tabar wiwi.
Sauran mutane shida da ake zargi sun haɗa da: Adamu, mai shekara 18, Hassan Abdullahi, mai shekara 20, Ibrahim Ibrahim, wanda aka fi sani da Bomboy, mai shekara 20, Usman Sale, wanda aka fi sani da Ado Gonja, mai shekara 21, Mohammed Salisu, wanda aka fi sani da RP Damboa, mai shekara 25, da Bako Mohammed, wanda aka fi sani da Balande, mai shekara 18, da ake zargin su da aikata mabanbanta laifuka.
Ya ƙara da cewa, dukkan waɗanda ake zargin mazauna unguwar Pompomari Sabon Kwalta ne, a cikin garin Damaturu. Inda ya ce a lokacin samamen, an gano wasu abubuwa da suka haɗa da tabar wiwi wasu abubuwa masu cutarwa, adda mai kaifi, wuƙa da kuma wasu abubuwa da ake kyautata zaton suna da alaƙa da ayyukan laifi.
Ana ci gaba da bincike don tantance waɗanda ake zargin ko suna da hannu a ayyukan laifi a cikin birnin da kuma gano waɗanda suke taimaka musu.










