Home SIYASA Abin da Obi ya Fada Kan Atiku – Dele Momodu

Abin da Obi ya Fada Kan Atiku – Dele Momodu

Momodu

Abin da Obi ya Fada Kan Atiku – Dele Momodu

 

Abuja – Daya daga cikin manya a jam’iyyar ADC, Dele Momodu, ya yi magana game da zaben shugaban kasa na 2027 a Najeriya.

Dele Momodu ya bayyana cewa Peter Obi ya taba kin amincewa da shawararsa ta hada kai da Atiku Abubakar a siyasa.

Abin da Obi ya fada kan Atiku Abubakar

Momodu ya ce Obi ya shaida masa cewa ya fi Atiku farin jini a tsakanin al’umma, cewar rahoton Punch.

Tsohon ‘dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa idan aka tambayi Obi, zai tabbatar bai yi masa karya ba ko kadan a kalamansa.

Momodu ya ce:

“Peter shi ne ɗan siyasa kaɗai da ya taɓa ziyartar gidana a London, Ghana da Lagos, a ɗaya daga cikin ziyarar, na gaya wa Peter cewa, ‘Ka yi ƙoƙarin yin aiki tare da Atiku.’

Momodu ya ce ya kawo misalin John Mahama na Ghana, wanda watakila da bai zama shugaban kasa ba da bai fara zama mataimakin Atta Mills ba.

Ya kuma kawo misalin Amurka, inda Joe Biden ya dawo ya zama shugaban kasa bayan ya nuna kwarewa duk da tsufansa.

“Na kuma ba shi misalin Amurka, inda duk da cewa Biden ya fi Obama shekaru sosai, amma daga baya ya dawo ya zama Shugaban Ƙasa saboda ya nuna ƙwarewa da cancantarsa.

“Kai dai ka taɓa zama gwamnan jiha ne kawai, amma Peter ya gaya mini cewa ya fi Atiku farin jini. Na rantse da Ubangiji. Idan ka gan shi, ka tambaye shi ko na yi masa ƙarya.”

A cewarsa, Obi ya taba zama gwamnan jiha ne kawai, amma ya dage yana ikirarin cewa ya fi Atiku karbuwa a idon jama’a, cewar Daily Post.

Momodu ya kuma yi tsokaci kan yanayin siyasar kasar, yana cewa akwai masu ruwa da tsaki da dama da ke fargabar karuwar tasirin Tinubu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Sojoji sun kama Mutane Biyu da ake zargin Ƴan kungiyar ISWAP ne a Borno da AdamawaSojoji Sun Ceto Mutane 22 da Aka yi Garkuwa da su, Sun Kwato Babura 3 a Jihar NejaA Legas, Hukumar Kwastam Ta Kwato Naira biliyan 2, Ta Kuma Kama Buhunan Shinkafa 21,000 Cikin Watanni TaraFRSC ta Musanta Zargin Ba da Guraben Daukar Aiki 50 ga Mazabar Ɗan Majalisa na GombeYadda Dalibai da Malamai da Aka Sace a Oyo Suka Tsira Bayan Kwanaki 56 a Hannun Masu Garkuwa – Shaida Ta DSSGwamnatin Tarayya ta Dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai da Ake ZargiHukumar NSCDC ta Binciki Mutuwar Mutane Sama da 30 da ake Zargi da Haƙar Ma'adinai ba Bisa ƙa'ida ba a Jihar NejaHauhawar Farashi a Najeriya ya Sauka Zuwa Kashi 15.39% a Watan Agusta – NBSHukumar Kwastam ta Kama Kwantena 56 Dauke da Haramtattun Kaya Na Naira Biliyan N5.53 a Tashar Onne2027: Babu Bukatar Sauyi – Oba na Benin ya yi Kira da a Sake Zaben TinubuGwamnatin Anambra Ta Fitar Da Takardun DMO, Ta Ce Obi Ya Bar Bashi Na Dala Miliyan $123.7Hukumar Kwastam ta Gurfanar da Mutum 3 a Gaban Kotu Bisa Zargin Safarar Namun Daji a KanoSojoji Sun Kai Farmaki Kan Ƴan Ta'adda a Kebbi, Sun Kashe Mutum Biyu a Neja, Sun Kwato MakamaiDr Lawan Sani: Yadda Masanin Tsaron Intanet Ya Zama Sarkin Gumel: Daga Shuaib S. AgakaAllah ne Kawai Zai Iya Hana Tinubu Cin Nasara a 2027 — Datti
X whatsapp