Shugaban Kasar Amurka ya Saka Hannu Kan Odar Zartarwa ta Kasuwancin Crypto

Shugaban Kasar Amurka ya Saka Hannu Kan Odar Zartarwa ta Kasuwancin Crypto

 

Wata sabuwa odar zartarwa wacce Shugaba Joe Biden ya sanya wa hannu ta ba da cikakken hasken sauyin rayuwa ga ‘yan crypto a Amurka.

Odar ta zartarwa ta yi kira ga hukumomin gwamnati a Amurka da su dauki matsaya daya kan crypto da sauran kadarorin intanet.

An sami rahotannin cece-kuce a fadar White House tsakanin ma’aikatar kudi da jami’an fadar White House game da shirin aiwatar da wannan manufa.

Joe Biden, shugaban kasar Amurka ya nuna alamar wani yunkuri na kafa tarihi a kasuwancin crypto a Amurka da ma duniya baki daya, matakin da masana suka yi hasashen zai kawo sauyi a duniyar crypto.

An ce hakan zai kawo sauyi ne a cikin tsari mai tsawo da ake ta tsammani, wanda ya zama damuwa a duniyar crypto, yawanci saboda al’amurran da suka shafi ka’idojin kudi a duniya kasancewar ana ganin crypto a matsayin sabon nau’in kudi, a cewar wani rahoto na CNBC.

Nesa ta zo kusa

An samu labarin rashin fahimta a fadar shugabancin Amurka ta White House tsakanin jami’ai da sakatariyar baitulmalin kasar, Janet Yellen wanda hakan ya haifar da koma baya wajen tabbatar lamarin.

Ya zuwa yanzu dai an samu abubuwa sun fara daidaita, domin kuwa bayanai game yiwuwar tabbatar da odar zartarwar za ta kankama bayan sanya hannu.

A karshe Shugaba Biden ya sanya hannu kan hakan a ranar Laraba, 9 ga Maris, 2022, yana mai kira ga hukumomi da su dauki hanyar da ta dace ta doka da sa ido kan kudaden intanet, in ji wata takarda daga fadar White House.

Abin da ya kamata ku sani game da lamarin

Lamarin dai zai mayar da hankali kan manyan fannoni guda shida: Kariyar kwastomomi da masu saka hannun jari, wadatar kudi, dakile haramtaccen ciniki da ayyuka munana, gogayyar Amurka a fagen a fadin duniya, hada-hadar kudi da kirkira mai ma’ana.

Kange masu siye daga hadari da zamba shine muhimmin sashi na tsarin. Mutane da yawa sun tafka faduwa a kasuwar crypto, hakazalikan an damfare su, kana sun yi asarar makudan kudade ta hanyar kutse ‘yan tsatsuba.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 18 hours 15 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 41 minutes 40 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here