Home Taska Kyautar da Fasinja ya Bawa Direban NAPEP Bayan Dawo Masa da Wayoyinsa...

Kyautar da Fasinja ya Bawa Direban NAPEP Bayan Dawo Masa da Wayoyinsa Guda 10

Kyautar da Fasinja ya Bawa Direban NAPEP Bayan Dawo Masa da Wayoyinsa Guda 10

 

Gaskiyar wani direban keke napep ya ya narkar da zukatan jama’a a shafukan sada zumunta tare da sanya jama’a cikin mamaki.

Direban dan Najeriya ya gano cewa wani fasinja ya manta wata jaka dauke da sabbin wayoyi guda 10 a cikin kekensa, inda ya yi kokarin gano mai shi.

A wani faifan bidiyo da ke zagayawa a intanet, a karshe ya gano mai jakar kuma an ba shi kyautar N1k kadai.

Wani fasinja ya cika da mamaki bayan da wani abin da ya manta a cikin keken napep ya dawo hannunsa sanadiyyar direban keke napep mai kyawun zuciya.

Wani shafin Instagram @gossipmilltv ya watsa wani faifan bidiyo da ke nuna lokacin da direban keken ya gano mai jakar da ke dauke da sabbin wayoyi guda 10 da sauran kayayyakin da ya manta lokacin da ya hau kekensa.

A cewar direban mai gaskiya, ya yi kokarin gano mai kayan ne bayan da ya gano jakar mai dauke kayayyaki a cikin abin hawansa.

A karshe ya yi nasara da bincikensa.

Direban ya samu kyautar kudi

Yayin da ‘yan kallo suka yaba masa da ya mayar da kayan da ba nasa ba, direban cikin murmushi ya ce duk da cewa shi mashayin giya ne, sata abu ne da ba zai taba yi ba.

Legit.ng ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a garin Aba na jihar Abia.

An ce an baiwa direban kyautar N1k ne kadai saboda gaskiyarsa.

Martanin ‘yan soshiyal midiya

@hype_frosh ya ce:

“Shima mutumin bai da kudi, abun da yake da shi shine dubu daya idan yana da abun da ya fi hakan zai basa don nuna godiya kan dawo da wayoyi da ya yi, dan uwa Allah ya shi maka albarka.

@cruiseloadedblog ya ce:

“Dukkan ku masu cewa dubu daya idan mutumin bai da abun da ya fi dubu daya sai ya kashe kansa, duk yakamata ku koyi yadda ake alkhairi ba tare da sa ran samun tukwici ba.

@queenseyyxo said:

“Nasan zai koma gida ya yi kwanaki 40 babu bacci yana mamakin dalilin da yasa ya dawo da wayoyi masu kyau a ranar.”

@temmiehairlyn ya ce:

“Amma ba shi 1k ya danyi wani banbarakwai haka’:…………. Kuma ka manta wayoyi guda 10, ba ka kyauta ba oooo.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp