Home WASANNI PSG ta Sha Kashi a Gidan Monaco a Gasar Ligue 1

PSG ta Sha Kashi a Gidan Monaco a Gasar Ligue 1

PSG ta Sha Kashi a Gidan Monaco a Gasar Ligue 1

Paris St Germain ta sha kashi da ci 3-0 a gidan Monaco a gasar Ligue 1 karawar mako na 29 da suka fafata ranar Lahadi.

Wissam Ben Yedder ne ya fara cin kwallo a minti na 25 da fara tamaula, sannan Kevin Volland ya kara na biyu a minti na 68 daga baya Yedder ya kara na uku a bugun fenariti kuma na biyu da ya ci, saura minti shida su tashi daga fafatawar.

Koci, Mouricio Pochettino zai kara fuskantar kalubale a shirin da yake na lashe kofin babbar gasar Faransa ta bana, bayan da Real Madrid ta fitar da PSG daga Champions League a kakar nan.

Pochettino ya maye gurbin Thomas Tuchel ranar 2 ga watan Janairu da nufin zai lashe Champions League, wanda kungiyar ke kishirwar kofin da bata taba dauka ba.

Shi kuwa Tuchel wanda ya koma Chelsea ranar 1 ga watan Janairun 2021 ya lashe Champions League a kakarsa ta farko da jan ragamar kungiyar Stamford Bridge.

Magoya bayan PSG kan yi wa Lionel Messi da Neymar ihu a wasan da suke yi a gida a baya bayan nan, sai dai kuma PSG a kwanan nan akwai damuwa kan rashin kokarin kungiyar a wasannin da take buga wa a waje, wadda ta yi rashin nasara a karawa hudun da ta yi.

Da wannan sakamakon PSG tana nan a matakinta na daya a kan teburin Ligue 1 da maki 65.

Sauran wasannin Paris Germain a kakar bana:

French Ligue 1 Ranar Lahadi 03 ga watan Afirilun 2022

Paris St-G.vLorient

French Ligue 1 Ranar Lahadi 10 ga watan Afirilun 2022

ClermontvParis St-G.

French Ligue 1 Ranar Lahadi 10 ga watan Afirilun 2022

Paris St-GermainvMarseille

French Ligue 1 Ranar Laraba 20 ga watan Afirilun 2022

Angers da Paris St-Germain

French Ligue 1 Ranar Lahadi 24 ga watan Afirilun 2022

Paris St-Germain da Lens

French Ligue 1 Ranar Lahadi 01 ga watan Mayun 2022

Strasbourg da Paris St-Germain

French Ligue 1 Ranar Lahadi 08 ga watan Mayun 2022

Paris St-Germain da Troyes

French Ligue 1 Ranar Asabar 14 ga watan Mayun 2022

Montpellier da Paris St-Germain

French Ligue 1 Ranar Asabar 21 ga watan Mayun 2022

Paris St-Germain da Metz

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Melaye Ya Kalubalanci Tinubu Zuwa Gasar Karatun Alqur'ani Bayan UmrahZaɓen 2027: Ƴan Sandan Najeriya da Birtaniya Sun Horas da Jami'ai 55 Don Haɓaka Ayyukan Yaƙi da Ta'addanciICPC ta Gargaɗi Jami'o'i da Kwalejojin Fasaha Kan Cin Hanci da Rashawa a Ayyukan TETFundGwamnatin Tarayya ta Sauya Dokar Kashe Gobara ta 1963 Zuwa Sabuwar Dokar CetoSojojin Ruwa da na Ƙasa Sun Kashe Ƴan Ta'adda 34 a Sabon Hari a Tafkin ChadiHukumar FRSC ta Kaddamar da Samame a Faɗin Ƙasa Kan Lambar Mota na BogiJama'ar Jigawa na Rera Taken "Dole Tinubu ya Tsaya" Yayin da Shugaban NITDA ke Jagorantar GangaminSanata Buba ya Kai Ta'aziyya ga Masarautar Misau Kan Waɗanda Suka Samu Hadari, Ya Kaddamar da Ofishin Yaƙin Neman Zaɓen Jam'iyyar PRPFBI ta Yabi Najeriya Kan Yakar Cin Zarafin Yara, Tinubu ya Yabawa Hukumar EFCCIGP Disu ya Samu Haɗin Kan Amurka da Italiya Don Horar da Ƴan Sanda 5000Kano: NSCDC ta Kai Samame Haramtacciyar Matatar Dizal, ta Kama Mutane 5Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta'adda 71 a Borno da YobeƳan Sanda Sun Tabbatar da Ceto Malamai 3 da Aka Sace a ZamfaraRahoton Siyasa: Rikicin Rijistar INEC da Zargin Sace Sowore Yayin da APC ta fi Ɗaukar HankaliNBSA ta Kaddamar da Sabon Tsarin Dijital Domin Magance Karancin Jini a Najeriya
X whatsapp