Home WASANNI Newcastle United na Son Daukar Neymar Daga PSG

Newcastle United na Son Daukar Neymar Daga PSG

Newcastle United na Son Daukar Neymar Daga PSG

 

An ruwaito cewar Newcastle United na duba hanyar da za ta dauko Neymar daga Paris St Germain a karshen kakar bana.

Newcastle wadda aka sayar da ita, ta saka kudi mai tsoka wajen sayo ‘yan wasan da za su kara karfin kungiyar, ciki har da dan kwallon Brazil, Neymar da take son dauka a karshen kakar nan.

Kamar yadda The Sun ta wallafa, Newcastle na bibiyar halin da Neymar ke ciki a PSG, tana kuma son yi masa tayin kudi mai tsoka, domin ya koma buga gasar Premier League.

Bayan da aka yi waje da PSG daga Champions League a bana a hannun Real Madrid, magoya bayan kungiyar Faransa kan yi wa wasu ‘yan wasan ihu a lokacin da suke buga mata leda, ciki har da Neymar.

Tun farko Neymar bai samu alaka mai kyau da PSG da kuma magoya bayanta ba, duk da kwazon da yake yi wa kungiyar, hakan ne Newcastle taga ya dace ta yi wa dan wasan Brazil tayin kudi mai tsoka, watakila ya samu buga babbar gasar tamaula ta Ingila cikin natsuwa.

Neymar yana da kunshin yarjejeniya da PSG wadda za ta kare a karshen kakar 2025, ana kuma ganin Newcastle za ta iya biyan albashin dan wasan na Yuro 500,000 duk mako idan ya amince ya koma kungiyar da taka leda.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp