• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home DUNIYA Da alama Lionel Messi zai kafa tarihi a gasar Copa America
  • DUNIYA
  • General
  • Labarai
  • WASANNI

Da alama Lionel Messi zai kafa tarihi a gasar Copa America

By
Ibrahim Ibrahim Nafiu
-
July 10, 2024
Arewa Award

Duk da cewa Messi baya cikin kasashen Nahiyar Turai da ke fafatawa a gasar Euro 2024 amma hakan bai hana kara sabunta kansa da daukakar da yake da ita a idon duniya ba.

Ɗan wasan gaban Inter Miami Lionel Messi ya jagoranci tawagar Argentina zuwa wasan ƙarshe na gasar Copa America bayan ta doke Canada da ci 2-0.

Ɗan wasan mai shekaru 37 da haihuwa ya zura ƙwallo a minti na shida bayan an dawo daga hutun rabin lokaci bayan ɗan wasan gaba na Manchester City Julian Alvarez, ya fara ci wa Argentina a minti na 22 da fara wasa.

Wannan shi ne karo na shida cikin gasa takwas na baya bayan nan da Argentina ta kai matakin wasan ƙarshe a gasar, kuma Messi ya bayyana cewa burinsa a yanzu shi ne ya ga cewa Argentina ta lashe gasar.

Read Also:

  • Dalilin Tinubu na soke afuwar da Ya yiwa Maryam Sanda
  • Gwamnan Jihar Katsina ya samar sabuwar ma’aikata a jihar
  • Za’a samar da sabbin jihohi 6 a Nijeriya

Ya ce: ‘Ba abu ne mai sauƙi ba ne sake samun damar buga wasan ƙarshe ba, don sake fafatawa don zama zakara’.

Wasan ƙarshen da za su fafata da Uruguay ko Colombia, zai kasance wasan ƙarshe da Angel di Maria zai buga wa Argentina kafin ya yi ritaya daga buga wasa sannan kuma har yanzu akwai shakku kan makomar Messi.

Amma kocin tawagar Argentina Lionel Scaloni ya ce zai yi ƙoƙarin shawo kan Di Maria da Messi su ci gaba da bugawa Argentina wasanni.

‘Batun Leo kusan iri ɗaya ne da na Angel,’ in ji Scaloni.

“Dole ne mu bar shi ya yanke ta shi shawarar kuma ba za mu taba zama wadanda za su rufe kofa ba, zai iya kasancewa tare da tawagarmu har tsawon lokacin da yake so. Kuma idan yana so ya yi ritaya amma duk da haka ya zo ya ci gaba da tallafa mana a wani mataki, abu ne da za mu yi maraba da shi’.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
  • TAGS
  • Argentina
  • Leonal Messi
  • wasanni
Previous articleKawu Sumaila ya gabatar da kudirin kirkirar sabuwar Jihar Tiga
Next articleKotun Koli ta haramtawa Gwamnatocin jihohi rike kudaden kananan hukumomi
Ibrahim Ibrahim Nafiu

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Dalilin Tinubu na soke afuwar da Ya yiwa Maryam Sanda

Gwamnan Jihar Katsina ya samar sabuwar ma’aikata a jihar

Za’a samar da sabbin jihohi 6 a Nijeriya

Jami’ar ABU ta musanta labarin samar da makamin Nukiliya

Mayakan Boko Haram sun fara kai hari da jirage marasa matuki a Borno

Babu wasu bayanan an yi wa masu bin wani addini kisan ƙare dangi – Sultan

Za ayi bincike kan masu laifin da Tinubu ya yiwa Afuwa

Tinubu ya taya Kwankwaso munar cika shekaru 69 a duniya

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da Amupitan a matsayin shugaban INEC

NAHCON ta bayyana dalilian da suka saka Saudiya rage mata kujerun aikin hajji bana

Dalilin da ya sa Amnesty ke neman a soke hukuncin kisa a Najeriya

Gwamnan jihar Bayelsa, ya fice daga jam’iyyarsa ta PDP.

Recent Posts

  • Dalilin Tinubu na soke afuwar da Ya yiwa Maryam Sanda
  • Gwamnan Jihar Katsina ya samar sabuwar ma’aikata a jihar
  • Za’a samar da sabbin jihohi 6 a Nijeriya
  • Jami’ar ABU ta musanta labarin samar da makamin Nukiliya
  • Mayakan Boko Haram sun fara kai hari da jirage marasa matuki a Borno

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1595 days 2 hours 49 minutes 58 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1577 days 4 hours 31 minutes 23 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
Dalilin Tinubu na soke afuwar da Ya yiwa Maryam SandaGwamnan Jihar Katsina ya samar sabuwar ma'aikata a jiharZa'a samar da sabbin jihohi 6 a NijeriyaJami'ar ABU ta musanta labarin samar da makamin NukiliyaMayakan Boko Haram sun fara kai hari da jirage marasa matuki a BornoBabu wasu bayanan an yi wa masu bin wani addini kisan ƙare dangi - SultanZa ayi bincike kan masu laifin da Tinubu ya yiwa AfuwaTinubu ya taya Kwankwaso munar cika shekaru 69 a duniyaMajalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da Amupitan a matsayin shugaban INECNAHCON ta bayyana dalilian da suka saka Saudiya rage mata kujerun aikin hajji banaDalilin da ya sa Amnesty ke neman a soke hukuncin kisa a NajeriyaGwamnan jihar Bayelsa, ya fice daga jam'iyyarsa ta PDP.Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta amince da naɗin Joash AmupitanGwamnatin Najeriya ta cire darasin Lissafi cikin sharuɗan samun gurbin karatun Jami'a ga wasu ɗalibanGwamnan Enugu ya koma APC bayan ficewa daga PDP
X whatsapp