Rikicin Rasha da Ukraine: An Dakatar da Haska Wasannin Premier Rasha
Hukumar shirya gasar Premier ta dakatar da yarjejeniyarta da Rasha na haska gasar sakamakon mamayar da Rashan ta yi wa Ukrain me makwabtaka da ita.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Wannan mataki zai fara aiki ne nan take, wanda hakan ke nufin ba za a haska wasanni hudun da za a yi ba a gasar ranar Alhamis.
An yanke hukuncin ne cikin minti 15 na tattaunawar da aka yi ta sa a hudu da rabi da duka kungiyoyin gasar 20 a Landan a ranar Talata.
Za a bayar da taimakon fan miliyan daya domin taimakawa mutanen Ukraine.











