Home Bincike Bincike: Shin da gaske ne mawallafin jaridar sahara reporters Sowore ya kaiwa...

Bincike: Shin da gaske ne mawallafin jaridar sahara reporters Sowore ya kaiwa NSA ziyara ta musamman a Yola da ke Jihar Adamawa?

Iƙirari: wani Faifen Bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta na zamani, da ke nuna tsohon dan takarar shugaban ƙasa kuma mawallafi a Jaridar Sahara Raporters Omoyele Sowore, ya kaiwa mashawarci na musamman ga Shugaban ƙasa kan harkokin tsaro (NSA) Nuhu Ribado ziyara a gidansa dake Yola, a jihar Adamawa domin yiwa shugaban kasar aiki a boye kamar yadda rubutun da aka haɗa da bidiyon ke cewa:

“kiran ‘yan siyasa matsayin abokan gaba, ba shi ke nuna cewa basu da wata alaƙa ba. Ka zama wayayye. Wannan Omoyele Sowore ne tare da Nuhu Ribadu, a gidan Ribadu dake garin Yola a jihar Adamawa, kada ka je ka hallaka kanka wajen yin faɗan da ba naka ba.”

A bidiyon, Sowore wanda ya sami rakiyar wasu mutane, an hange shi yana gaida Ribadu cikin girmamawa. Yana Magana cikin tattausar murya dake cewa: “nayi farin cikin ganin Ka Nuhu Ribadu, yanzu dai gani a Yola- ji nake ni ma tamkar gida na……

Nuhu Ribadu, sanye da fararen kaya da bakar Hula cikin raha yake gaida tsohon dan takarar,” yayin da ya ke ƙoƙarin rungume shi.

Yayin da suke shirin shiga cikin ginin gida, shi kuwa Sowore ke kokarin budewa Rubadu kofa cikin girmamawa.

Iƙirarin ya yamutsa hazo, tare da wasu tambayoyi kan Sowore, da ake masa kallon tsayayye, kuma jajirtacce.

Omoyele Sowore da aka sani da tsayawa tsayin daka wajen kalubalantar ‘yan siyasa da Shuwagabannin Nijeriya, wanda ya samar da wani bigire da a bayyane yake kuma ba’a sauya masa tunani.  Ya mayar da kan sa mai kalubalantar masu riƙe da madafun iko, ta hanyar yin amfani da kalamai irin su masu cin hanci, rashin iya mulki da bayyana gazawarsu wajen tafikas da Nijeriya.

Tabbatar da shahihancin labara: PRNigeria ta gudanar da bincike ta hanyar yin amfani da hanyar bincikar hoto ta (reverse vedio search). Da wasu hanyoyi, cikin su har da bidiyon da aka dora a manhajar YouTube  da ma’adanar Sahara Reporters, an gano cewa an wallafa bidiyon ne a farko-farkon shekarar 2018. Wannan ya faru ne lokacin da Sowere yaje yakin neman zabe a jihar Adamawa karkashin inuwar Jam’iyyar (AAC).

Bidiyon da sahara TV ta dora wanda ya nuna Sowore a kan hanya in da yake cewa Ribadu “Yola tamkar gida yake a waje na” domin na yi hidimar kasa a shekara 1994/95, kamar yadda bincike ya tabbatar.

Wani abu mai kama da wannan kuma an bincike shafin Sowore na X wanda aka fi sani da twitter da facebook, ya nuna babu wata shaida da ta bayyana cewa ya ziyarci Yola ko ya yi wata ganawa tare da Nuhu Ribadu.

Sai dai:

Kwanaki biyar da suka gabata an hango shi a wajen taron bikin tunawa da haihuwar matar tsohon ɗantakarar shugabancin ƙasa a kakar zaben 2023 karkashin inuwar jam’iyyar SDP.

A ranar 25 ga watan Afrilun  yayi wasu kalaman Allah wadai kan yadda ake amfani da siyasa wajen danne na ƙasa, bisa tafiyar da yake son yi, a babbar kotun tarayya ta Abuja, a wani yunkuri na karbar Passport din sa da mai shari’a MS liman ya bayar da damar karbewa.

Nan kusa-kusa an hango Sowore yana ganawa da kafafen yaɗa labarai na gida da na waje kan abin da ya shafi tsaro da cigaban matasa, wanda kuma ba’a ji ya ambaci NSA ko kuma Adamawa ba.

A hannun guda, rahotannin daga kafafen yada labarai masu inganci da suka hadar da The Nation, Premium Times, da Channels TV sun tabbatar da cewa Rubadu yana:

 Jihar Benuwai a ranar 22 ga watan Afrilu, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin jajantawa waɗanda harin makiyaya ya rutsa da su.

A ranar 24 ga watan na Afrilu, ya gana da Defence Intelligence Agency (DIA) a birnin tarayya Abuja, wanda kuma aka fitar da takardar manema labarai kan matakan da aka dauka a fannin tsaron.

Babu wani sahihin labari da ya tabbatar da cewa Ribado ya ziyarci Yola a cikin makwannin nan.

Wadannan bayanai da labaran ayyuka sun bayyana cewa Ribadu yana Abuja da benuwai, ba jihar Adamawa ba.

Kammalawa: PRNigeria ta gano cewa bidiyon da aka yada na Omoyele Sowore ya kai ziyara ga mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Nuhu Ribadu a gidansa dake birnin Yola ba na yanzu bane; bidiyo ne da aka dauka tun a shekarar 2018 lokacin da Sowore ya je yakin neman zaben a lokacin da ya nemi takarar shugabancin Nijeriya na farko  karkashin inuwa Jam’iyyar (AAC). Bincike kwanannan ya nuna cewa Ribadu yana  Benue da Abuja, shi kuwa Sowore yana Abuja, kuma wadannan bayanai an same su ne a shafukansu na sada zumunta da kuma kafafen yaɗa labarai.

Bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta na zamani, wanda babu cikakken bayani ya taimaka wajen yamutsa hazo a ‘yan tsakaninnan wanda kuma ya bawa Sowore matsala kasancewar yadda aka san shi da tsayawa tsayin daka wajen faɗin gaskiya da kalubalantar ƴan siyasa Nijeriya.

Hukunci: shashen bincike na PRNigeria ya yanke hukuncin cewa wannan bidiyon da aka saka babu cikakken bayani, an yi haka ne domin rikita mutane.

PRNigeria

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HURIWA ta Soki Ƴan Sanda da NDPC Kan Jinkirin Binciken Zargin Kutse da aka yi wa Bayanan NIPSS da ya Shafi Jami’in Sojan RuwaƳa'yan El-Rufai Sun Shiga Rikici Yayin da Bashir ya Zargi Bello da Shan Muggan Kwayoyi da Cin Amanar suTsaro, Fafutuka da Nauyin Tabbatarwa Daga Mukhtar Ya’u MadobiONSA ta Fitar da Faɗakarwar Tsaro, ta Bukaci Ƴan Najeriya su ƙara Yawan Tsawaita TsaroHukumar DSS ta Dakatar da Shari'ar Sowore Kan Laifukan Intanet Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa na 2027Gwarzo ya ba da Gudummuwar ₦10m ga Horarwa na Musamman na PRNigeria Bayan ya ba da Gidansa na Abuja Don Cibiyar Koyon Aikin Jarida2027: Bayan Takardu da Sauran Tsoffin Maganganu Marasa Amfani, ‘Yan Najeriya Sun Cancanci Kamfen Din da Ya Dace Da Matsaloli  Daga Kabir AkintayoGwamnati Tarayya ta Bayyana Bas 100 Masu Amfani da Wutar Lantarki Don Rage Wa Ma’aikatan Gwamnati Matsalar SufuriƳan Ta’adda na Amfani da Kafafen Sada Zumunta da Dandamalin Aikin Tura Kuɗi Don Tallafa Wa Ayyukansu — BukartiBinciken Gaskiya na PRNigeria: Ta Karyata Da’awar Tony Elumelu ta Cewa An yi Satar Man Fetur Kashi 97% Kafin Zamanin TinubuMeyasa Mutuwar Bazata Take Daukar Masu Alheri ta Bar Mugaye ? Na Yushau A. ShuaibSojoji Sun Kama Bindigar AK-103 Da Aka Boye a Cikin Jakar Gero, Sun Kama Mutum Uku A ZamfaraSojoji Sun Kama Shahararren Shugaban Ƴan Bindiga, 'Sanusi Maigilas' a Dajin Katsina2027: Yadda Zan Magance Rashin Tsaro, In Magance Matsalolin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Kwara — Zakari MohammedLabarin NIPSS Mai Damuwa: Lokacin da Jami'in Sojan Ruwa Ya Cin Zarafin Mawallafi Daga Nuhu Mohammed
X whatsapp