Home Bincike Bincike: Shin da gaske ne ‘Yanbindiga sun mutu a yankin kabilar Nufawa...

Bincike: Shin da gaske ne ‘Yanbindiga sun mutu a yankin kabilar Nufawa bayan sun yi garkuwa da mutane?

Ikirari: Wani faifen bidiyo da aka yada ta manhajar whatsapp ya nuna wasu mutane kwance da bundugu raye a wuyansu. Wanda a jikin bidiyon aka rubuta cewa, wadannan wasu ‘yan bindiga ne da suka yi garkuwa da wasu mutane ‘yan kabilar Nufe a jihar Kwara, cikin garin Lafiagi, amma cuka mutu cikin sa’oi 24 da yin garuwar.

A jikin  bidiyo an yi rubutun ne kamar haka:

“Wannan lamarin ya auku ne a yankin al’ummar dake Magana da yaren Nufanci a jihar Kwara, a garin Lafiagi. An yi garkuwa da al’ummar yankin kuma aka kai su wani waje da babu wanda ya sani. Amma cikin sa’oi ashirin da hudu, kawai sai masu garkuwar suka fara mutuwa daya bayan daya, kamar yadda aka bayyana a bidiyon. A sama ga  gyarren bidiyon cikin harshen nufanci.”

A bidiyon, PRNigeria ta gano abinda ake cewa cikin harshen nufanci. Bayan ta fassara ana cewa wannan masu garkuwa ne bayan su yi garkuwa da mutane sun kai su daji, da safe, suka fara mutuwa daya bayan daya, ba tare da sanin makasudin hakan ba.

Mai maganar ya kara da cewa wadanda lamarin ya rutsa da su sun fantsama cikin daji domin tsira da rayukan, don haka ya kamata mutane su taya su murna domin “Allah ya fara amsar Addu’oin su.” Ya kuma yi addu’ar kada ‘yan ta’addan su sake zuwa garin Nufawa.

Binciken sahihancin labara: domin tabbatar da sahihancin ikirain, PRNigeria ta gudanar da bincike kwakkwafi kan bidiyon inda ta raba shi sala-sala a manhajar “Reverse image searches”

Binciken ya nuna cewa hotunan dake cikin bidiyon ba daga jihar Kwara ya fito ba daga jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya yake.

Ya nuna mayakan Boko Haram ko ISWAP takwas da dakarun hadin gwiwa na CJTF da HF suka hallaka a garin Manawaji, dakekaramar hukumar Gamboru Ngala a jihar Borno. Sojojin sun sami nasarar hallaka mayakan bayan wani artabu da suka yi. Inda suka kwato makamai gami da alburusai.

Haka kuma wani bincike kan hotunan ya nuna shi matsayin hoton dake cikin hotunan da aka walafa a labarin nasarar da dakarun Operation Hadin kai suka samu a jihar Borno

Kammalawa: bidiyon dai na nuna hotunan mutum takwas na mayakan boko haram ko ISWAP da sojoji suka hallaka a jihar Borno bashi da wata alaka da jihar kwara.

Hukunci: ikirarin da ke cewa ‘yanbindiga sun mutum kwatsam a yankin da ake Magana da harshen Nufanci a jihar kwara bayan sun yi garkuwa da mazauna garin ba gaskiya bane, bidiyon da aka yi domin a karfafi hoton an yi shi ne da wata manufa

daga PRNigeria

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp