Home General Sojojin Najeriya – Mun hallaka ‘ƴan bindiga 792 cikin wata uku

Sojojin Najeriya – Mun hallaka ‘ƴan bindiga 792 cikin wata uku

Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce ta hallaka ƴan bindiga kimanin 792 tsakanin watan Yuli zuwa Satumban da muke ciki.

Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran hedkwatar, Edward Buba ya fitar, in da ya ce dakarun tsaron ƙasar, ƙarƙashin rundunar Operation HADIN KAI ta samu nasarar kai hare-hare cikin dajin Sambisa da na Tumbuns a yankin tafkin Chadi, tare da kashe wasu manyan kwamandojin ‘ƴan bindigar.

Sanarwar ta ƙara da cewa hare-haren da sojojin suka kai wa mayaƙan ya rage musu ƙarfi, tare da hana su ƙaddamar da manya-manyan hare-hare.

Edwar Buba ya ci gaba da cewa a lokacin ayyukan soji a waɗanann yankuna tsakanin waɗannan watanni, dakarun ƙasar sun samu nasarar kashe wasu manyan kwamandojin ƴanbingida da suka haɗa da Munzir Arika da Sani Dilla (Ɗan Hausawan Jubillaram) da Ameer Modu da Ɗan Fulani Fari Fari Dungusu da Abu Darda da Bakoura Arina Chiki da Dungusu da Abu Darda da kuma Abu Rijab.

Haka kuma sanarwar ta ce an kama wasu da ake zargi da kasancewa ƴanbidigar kimanin 606 tsakanin waɗannan watanni tare da kuɓutar da mutum 476 da ake garkuwa da su, sannan kuma wasu iyalan ƴanbindigar kimanin 7,283 suka miƙa wuya.

Sanarwar ta kuma ce dakarun sojin sun ƙwato makamai da suka haɗa da bindiga ƙirar AK47 guda 339, da ƙirar gida 58 da ƙananan bindigogi 83 da kuma tarin alburusai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp