Majalisar Dattawa ta amince da ba da umarnin kamo mata Manajan Daraktan Kamfanin Gine-gine na Julius Berger, Mista Peer Lubasch.
Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya ce ’yan majalisar sun ba da umarnin ne saboda sau uku Shugaban Kamfanin na kin amsa gayyatar majalisar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Majalisar ta gayyaci shugaban kamfanin ne kan zargin ƙara Naira biliyan 141 a kuɗin aikin babban titin Itukpani zuwa Itu da ke jIhar Enugu, tare da yin watsi da aikin.
Da yake gabatar da ƙudurin, Mai Tsawatarwan Majalisa, Sanata Osita Ngwu, ya zargi kamfanin da ƙara kuɗin aikin daga Naira biliyan 54 zuwa biliyan 195.
Dan majalisar ta bayyana cewa daga bisani kamfanin ya kwashe kayansa daga wurin da ake aikin.
A kan haka ne sau uku majalisar ta na gayyatar shugaban kamfanin na Julius Berger ya zo ya yi bayani, amma ya yi watsi da su.
PRNigeria hausa











