NMDPRA ta Gargaɗi Gidajen Man Kan Sayar da Farashin Fetur
Hukumar Kula da Harkokin ta Najeriya (NMDPRA) ta yi gargaɗin cewa za ta hukunta gidajen man da ke sayar da man fetur a farashin da bai yi daidai da farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, George Ene-Ita, ya fitar a ranar Laraba, ya ce hukumar na sane da raguwar farashin ɗanyen mai a duniya, inda ya ce dole ne farashin man fetur ya zo daidai da yadda farashin yake, kamar yadda dokar albarkatun mai ta 2021 a ƙasar ta tanada.
Ya ce hukumar ta riga ta gargaɗi kamfanonin kasuwancin mai da su guji ƙara farashi domin cin ribar da ta wuce ƙa’ida.
NMDPRA ta ce ana sa ido kan gidajen mai, kuma za a ɗauki matakin a kan duk wanda aka samu da laifi.
Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan kiran da ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya yi ga hukumomin da su ɗauki mataki kan dillalan man.
Ya ce bayan dakatar da yaƙi tsakanin Iran da Amurka, ƴan Najeriya na sa ran ganin an rage farashin man fetur a ƙasar.











