Yaɗa Farfaganda da ƙiyayya Kan Gwamnati ba Zai Kawo ƙarshenta ba – Matawalle
Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya buƙaci ƴan adawa da su daina yin abubuwan da ka iya tunzura ƴan Najeriya ko kuma ɓata sunan ƙasar a idon duniya.
A cikin wata sanarwa da kakakinsa Ahmad Dan-Wudil ya fitar, Matawalle ya ce abin takaici ne yadda ake zargin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ɗauki hayar kamfanonin kamun kafa na ƙasashen waje domin yaɗa tsofaffin takardu da suka shafi Shugaba Bola Tinubu a Amurka.
Ya ce hakan sam ba ya amfanar da dimokuraɗiyyar ƙasar.
Read Also:
“Maimakon ƙoƙarin ɓata sunan Najeriya da kuma ƙasƙantar da martabar ofishin shugaban ƙasa a ƙasashen waje, ya kamata ƴan adawa su mayar da hankali wajen tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar tsaro, ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma inganta rayuwar ƴan Najeriya,” in ji Ministan
Ya ce ofishin shugaban ƙasa na da martabarta, don haka ya kamata a mutunta shi duk da bambancin siyasa.
Matawalle ya kuma buga misali da yadda shugaban Amurka Donald Trump ya yaba wa Shugaba Tinubu kan jagorancinsa da kuma ƙoƙarin gwamnatinsa kan tsaro da yaƙi da ta’addanci.
Ministan ya ƙara da cewa yaɗa farfaganda da ƙiyayya kan gwamnati ba zai kawo ƙarshenta ba.
“Waɗanda suke tunanin cewa ƙarya da makirci za su kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu suna yaudarar kansu, domin Najeriya ta ƴan Najeriya ce, kuma su ne za su sake yanke hukunci a zaɓen 2027,” in ji sanarwar












