Mutane 2 Sun Mutu Bayan Hatsarin Tankar Mai a Ibadan
Hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo, ta tabbatar da mutuwar mutanen biyu, waɗanda suka maƙale a cikin tankar bayan aukuwar hatsarin.
Shugaban hukumar, Maroof Akinwande, ya ce hatsarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar a kusa da gidan Guru Maharaji, a kan babbar hanyar Ibadan zuwa Legas.
cewarsa, bincike ya nuna cewa birkin tankar ne ya samu matsala yayin da direban ke tafiya, lamarin da ya sa motar ta kauce daga kan hanya tare da kifewa.
Read Also:
Jami’an kashe gobara sun isa wajen domin ceto mutanen da suka maƙale a cikin tankar.
Sai dai sun gano cewa mutane biyun sun riga sun rasu.
Daga bisani jami’an suka fitar da gawarwakinsu tare da miƙa su ga Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC).
Wani ganau, ya ce man fetur ne ya fara malala daga tankar zuwa kan babbar hanyar, lamarin da ya sa wasu mazauna yankin suka fito ɗauke da bokiti da jarkoki domin kwasar man.
Sai dai jami’an kashe gobara sun ɗauki matakin gaggawa tare da shawo kan lamarin kafin wuta ta tashi a wajen.











